Home Back

Saudiyya na farautar Jesus da Partey daga Arsenal, Man Utd na shirin cefanar da Sancho

bbc.com 2024/5/19
jesus

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal na shirin karban tayi kan sayar da ɗan wasan gaba daga Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 27, a wannan kaka. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya daga Ghana Thomas Partey, mai shekara 30, da Jesus sun ja hankalin ƙungiyoyi da dama daga Saudiyya, inda ake ta gabatarwa Arsenal tayi mai kwaɓi a kan 'yan wasan biyu. (Express)

Ɗan wasan gaba a Newcastle Callum Wilson na cikin rashin tabbas yayinda ake alakanta shi da barin St James' Park. (Mirror)

Kocin Bayern Munich mai shirin bankwana Thomas Tuchel shi aka fi tunanin zai maye gurbin sabon koci a Manchester United da kocinta Erik ten Hag ke shirin tafiya. (Football Insider)

Borussia Dortmund na son riƙe ɗan wasan Ingila da ke zaman aro da ita, Jadon Sancho, mai shekara 24, zuwa kaka ta gaba, sai dai da wahala ta iya daidaitawa kan yarjejeniyar dindindin da Manchester United. (Sky Sport Germany)

Manchester United na fatan samun fam miliyan 100 a cinikin Sancho da Mason Greenwood mai shekara 22 a wannan kaka. (Give Me Sport)

Ɗan wasan gaba a Stuttgart daga Guinea Serhou Guirassy, mai shekara 28, ya kasance wanda kocin Arsenal Mikel Arteta ke farautar a kokarin inganta 'yan wasansa na gaba. (Fichajes - in Spanish)

Kalvin Phillips da ke buga tsakiya daga Ingila na fatan komawa Leeds United a wannan kaka, sai dai ya danganta da kudaden da zai samu.(Football Insider)

Aston Villa na gab da saye ɗan wasan Atletico Madrid Mario Hermoso, mai shekara 28. (AS - in Spanish)

AC Milan ta shirin gabatar da cinikin kan ɗan wasan nan mai shekara 24 daga Canada Jonathan David na Lille a wannan kaka. (Calciomercato - in Italian)

People are also reading