Rikicin Siyasar APC Ya Dawo Sabo, Sanatan Zamfara Ya Farfado da Wani Tsagin Jam’iyyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Jigon APC a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya sanar da dawowar shugabancin wani tsagin jam'iyyar yayin da rikicin cikin gida ya sake mamaye APC a jihar.
Sanata Marafa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da daruruwan magoya bayansa da suka yi takanas daga Zamfara suka ziyarce shi a Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsagi biyu ne ke gudanar da shugabancin APC a Zamfara tun bayan da rikici ya balle a jam'iyyar lokacin gwamnatin Yari da kuma Matawalle.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar tarayya ta 7 da ta 8 ya ce yanzu ya farfado da tsagin da yake jagoranta saboda an cire shi da magoya bayansa daga tarurrukan jam'iyyar na baya-bayan nan a jihar.
Ya amince cewa rikicin jam'iyyar ne ya kai ga faduwarta babban zaben jihar, in aka cire na shugaban kasa, lokacin da yake jagorantar kungiyar yakin zaben Tinubu/Shettima.
Amma da yake tsame kansa daga rikicin jihar, ya karyata masu jita-jitar cewa tsaginsa ne ya shigar da APC kara a kotu a shekarar 2019, in ji rahoton jaridar Guardian.
Sanata Marafa ya bayyana cewa jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ka'ida ba, kuma aka garzaya kotu domin bin kadin lamarin.
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Tukur Danfulani, ta fara shirin dinke barakar da take fama da ita.
Jam’iyyar ta APC ta yanke shawarar gudanar da taro na wata-wata da nufin hada kan dukkanin mambonta ta yadda za su zama tsintsiya madaurinki daya.
Asali: Legit.ng