Home Back

Tinubu Ya Samu Tazarce, an Zabe Shi Matsayin Shugaban ECOWAS Karo Na 2

legit.ng 2024/10/5
  • Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya samu tazarce kan kujerar shugaban kungiyar ECOWAS a taron kungiyar na 65
  • Taron wanda ya gudana a Abuja ya samu halartar shugabannin kungiyar ECOWAS inda suka sake zabar Tinubu karo na biyu
  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin kasashen ECOWAS da su ba da gudunmawar kudi wajen yaki da rashin tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An sake zaben shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), kimanin shekara guda bayan ya karbi ragamar shugabancin kungiyar.

An sake zaben Tinubu matsayin shugaban kungiyar ECOWAS a babban taron kungiyar karo na 65 da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a yau Lahadi.

ECOWAS ta zabi sabon shugabanta a babban taronta na 64
Abuja: Tinubu ya zama shugaban ECOWAS karo na biyu. Hoto: @ecowas_cedeao Asali: Twitter

ECOWAS ta dauki salon yaki da tsaro

A jawabinsa na bude taron, Shugaba Tinubu ya bukaci kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS da su yi hadakar kudi domin taimakawa yaki da ta’addanci inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yayin da muke yunkurin fara aiki da rundunar ESF ta ECOWAS wajen yaki da ta'addanci, dole ne in jaddada cewa nasarar wannan shirin na bukatar kudi daga gare mu.
“Don haka dole ne mu tabbatar cewa mun cimma shawarwarin da ministocin tsaro da na kudi suka gindaya domin dakile matsalar rashin tsaro a yankinmu."

Wa'adin Tinubu a shugaban ECOWAS ya kare

Tun da fari, mun ruwaito cewa a yau Lahadi ne wa’adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ya zo karshe.

Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya, kungiyar ECOWAS ta amince da Bola Tinubu matsayin shugabanta a 2023.

Wannan mukami ya zo wa Tinubu da gardama sakamakon matsalolin da suka dinga faruwa a wasu kasashen ECOWAS musamman wadanda aka yi juyin mulkin gwamnati a cikinsu.

Asali: Legit.ng

People are also reading