Tinubu Ya Samu Tazarce, an Zabe Shi Matsayin Shugaban ECOWAS Karo Na 2
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An sake zaben shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), kimanin shekara guda bayan ya karbi ragamar shugabancin kungiyar.
An sake zaben Tinubu matsayin shugaban kungiyar ECOWAS a babban taron kungiyar karo na 65 da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a yau Lahadi.
A jawabinsa na bude taron, Shugaba Tinubu ya bukaci kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS da su yi hadakar kudi domin taimakawa yaki da ta’addanci inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yayin da muke yunkurin fara aiki da rundunar ESF ta ECOWAS wajen yaki da ta'addanci, dole ne in jaddada cewa nasarar wannan shirin na bukatar kudi daga gare mu.
“Don haka dole ne mu tabbatar cewa mun cimma shawarwarin da ministocin tsaro da na kudi suka gindaya domin dakile matsalar rashin tsaro a yankinmu."
Tun da fari, mun ruwaito cewa a yau Lahadi ne wa’adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ya zo karshe.
Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya, kungiyar ECOWAS ta amince da Bola Tinubu matsayin shugabanta a 2023.
Wannan mukami ya zo wa Tinubu da gardama sakamakon matsalolin da suka dinga faruwa a wasu kasashen ECOWAS musamman wadanda aka yi juyin mulkin gwamnati a cikinsu.
Asali: Legit.ng