Rikicin Sarauta: Gwamna Abba Na Cikin Matsala, An Bayyana Sahihin Sarkin Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Law Mefor, fitaccen mai sharhi kan al'amuran yau da kullumal ya ce gwamnatin jihar Kano ba ta ikon sauya hukuncin da kotu ta yanke.
Mefor ya bayyana cewa idan gwamnatin Abba Kabir tana da ja da hukuncin babbar kotun tarayya, kamata ya yi ta ɗaukaka ƙara ba wai ta take umarnin doka ba.
Idan baku manta ba babbar kotun tarayya ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, Mai shari'a Abdullahi Liman ya soke duka matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka bayan kafa sabuwar dokar masarauta.
Alkali Liman ya ce hukuncin bai shafi dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita ba.
Amma ya soki Gwamna Abba bisa yadda ya zartar da dokar kuma ya mayat da Sanusi II a watan Mayu duk da kotun ta umarci ya jinkirta.
Da yake martani kan ruɗanin sarautar Kano a wata hira da Arise tv, Mefor ya ce:
"Kotun ɗaukaka ƙara ce kaɗai ke hurumin jingine umarnin kotu ko ta tabbatar da shi, amma ba gwamnan jihar Kano ba, amma gwamnan ya s aƙafa ya shure umarnin kotu.
"Haka majalisar dokokin jihar ta mara masa baya, suka zartar da wannan doka ta masarauta, wanda yanzu tana kasa tana dabo."
A wani rahoton na daban hukuncin babbar kotun tarayya a shari'ar sarautar Kano ya haddasa saɓani tsakanin hadimin gwamna da lauya Abba Hikima.
Mai magana da yawun Abba Kabir ya ce hukuncin ya rusa masarautu biyar yayin da Hikima ke ganin har yanzu Aminu Bayero ne Sarkin Kano.
Asali: Legit.ng