Ɗalibai sama da 100 ne a ka sace a Kaduna ranar Alhamis, gwamnati, Ƴansanda basu ce komai ba
Ƴanbindiga sun sace ɗalibai sama da 100 a makarantar Firamare dake Kuriga, Ƙaramar Hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa an sace ɗaliban ne a daidai suna Asambili za su shiga ajujuwa.
An ce ƴanbindigan sun zagaye makarantar ne suka sace ɗaliban kaf ɗin su.
PREMIUM TIMES ta nemi ji daga runduna ƴansandan jihar, ba su maida kira da ak yi wa kakakin rundunar ba.
Haka kuma shima kwamishinan tsaron jihar, Samuel Aruwan, bai amsa kira sa aka yi masa ba domin ƙarin bayani a kai.