Home Back

“Jima’i Kadai Ke Rage Mana Kunci”: ’Yan Gudun Hijira Sun Cika Sansani da Jarirai

legit.ng 2024/6/26
  • Yayin da ake cikin wani hali a sansanonin gudun hijira a jihar Benue, ma’aurata na ci gaba da kyankyashe jarirai
  • Hukumomi musamman na lafiya sun koka kan yadda ake samun karuwar yawan haihuwa duk da matsalolin da ke ciki
  • Akalla an samu haihuwar jarirai 200 a cikin wata daya wanda ma’auratan suka ce hakan na rage musu kunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue – An yi ittifakin jihar Benue na dauke da sansanin ‘yan gudun hijira akalla 17 da mutane 1.5m a cikinsu.

Mafi yawan wadanda ke sansanin an koro su ne daga garuruwansu kan rashin tsaro da ya addabi jihar baki daya.

Hanakalin hukumomi ya tashi bayan 'yan gudun hijira sun cika sansani da jarirai
Ana yawan samun karuwar jarirai a sansanin gudun hijira a jihar Benue. Asali: Original

Benue: Tulin matsaloli a sansanin gudun hijira

Vanguard ta tattaro cewa wadanda ke rayuwa a sansanin na fuskantar matsaloli da suka hada da rashin isasshen abinci da magani da kuma wurin kwana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai duk da matsalolin da suke fuskanta bincike ya tabbatar da yawan samun karuwar haihuwa a sansanin.

Duk da halin da ake ciki na matsaloli, mazaje ba su gajiya wurin kusantar matansu domin hayayyafa, cewar Leadership.

Hukumomi sun fara korafi musamman bangaren lafiya kan yadda ake kara haihuwa madadin kayyade iyali a sansanin.

Hukumomin suna kokawa kan rashin tabbas na ‘ya’yan da ake haihuwa duba da rashin ingantaccen lafiya da kuma abinci.

Yawan jarirai a sansanin gudun hijira

Akalla an haifi jarirai 200 cikin wata daya kacal wanda ya tayarwa masu kula da sansanonin hankali duk da kokarin da suke yi na tallafawa.

Wani mazaunin sansanin, Anngu ya ce hakan yana rage musu kunci duk lokacin da suka kwanta da matansu saboda nishadi.

“Babu wanda zai hana mu jin dadi da matanmu kawai domin muna sansanin gudun hijira duk da wasu mazan ba su son haihuwa.”
“Na zo nan shekaru biyu da suka wuce amma ina amfani da kariyar daukar ciki wanda hukumomi suke bamu, amma gaskiya wasu ba su amfani da shi.”

- Anngu

Sakatariyar hukumar lafiya matakin farko a jihar, Grace Wende ta nuna damuwa kan yadda ake kara haihuwa a sansanin gudun hijira.

Grace ta ce dole gwamnati za ta yi abin da ya kamata domin tabbatar kawo tsari wanda zai rage yawan haihuwa a sansanonin.

Benue: Kotu ta hana Alia bincikar Ortom

Kun ji cewa wata kotu a jihar Benue ta haramtawa Gwama Alia Hyacinth bincikar Samuel Ortom a jihar kan badalaka.

Kotun ta ba da umarnin ne bayan korafin da lauyan tsohon gwamnan ya shigar inda ta bukaci dakatar da binciken.

Asali: Legit.ng

People are also reading