Home Back

'Yansanda na ci gaba da afka wa masu bore a Kenya

dw.com 5 days ago
Wasu masu zanga-zanga a Kenya
Wasu masu zanga-zanga a Kenya

Rahotannin da ke fitowa daga Nairobi babban birnin kasar Kenya, na cewa 'yansanda na can suna harbe-harben barkonon tsohuwa da harsasan rona a kan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba William Ruto.

Masu boren dai sun sake karade manyan titunan kasar ta Kenya ne a yau Alhamis, duk da cewa shugaban kasar ya ba da umurnin janye karin harajin da ya haddasa tarzomar da ta kai ga mace-mace.

Matasan Kenya wadanda su ne galibi ke boren, sun ce ba za su janye ba saboda su ba su yarda Shugaba William Ruto zai iya kare masu makomarsu ba.

A shekaran jiya Talata ne dubban matasan suka kona majalisar dokoki, a daidai lokacin da 'yan majalisa suka amince da dokar karin haraji da Shugaba Ruto ya gabatar.

People are also reading