Home Back

Gwamnatin Tarayya ta yi hayar dillali daga Amurka, wanda zai yi mata gwanjon tsoffin Jiragen Shugaban Ƙasa guda uku

premiumtimesng.com 5 days ago
Gwamnatin Tarayya ta yi hayar dillali daga Amurka, wanda zai yi mata gwanjon tsoffin Jiragen Shugaban Ƙasa guda uku

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki hayar wani dillali mazaunin Amurka, domin ya kaɗa mata gwanjon sayar da wasu Jiragen Fadar Shugaban Ƙasa guda uku, waɗanda sun shafe shekara da shekaru ana zirga-zirga da su.

A naɗa JetHQ a matsayin kamfanin dillancin yi wa jiragen gwanjo, su uku, da suka haɗa da Boeing 737 Boeing Business Jet (BBJ), wanda a cikin sa ne Shugaban Ƙasa ke karakaina a ciki, sai kuma wani samfurin Gulfstream da kuma ƙirar Falcon 7×.

JetHQ zai yanka wa jiragen uku farashi, sannan kuma ya tallata su, kuma ya sayar ga duk mai buƙata.

Wani jami’in da aka tattauna da shi, ya ce za a yi amfani da kuɗin da aka sayar da jiragen wajen yin ciko domin sayen wasu sabbi.

A farkon makon nan ne Majalisar Dattawa ta goyi bayan a gaggauta sai wa Tinubu da Shettima sabbin jiragen, sun ce rayuwan Shugaban Ƙasa na cikin haɗari.

Kwamitin Harkokin Tsaron Ƙasa na Majalisar Dattawa, ya bi ra’ayin Kwamitin Tsaron Ƙasa na Majalisar Tarayya, inda shi ma ya goyi bayan a gaggauta sayen sabbin jiragen sama ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da Mataimakin sa, Kashim Shettima.

Shugaban Kwamiti Shehu Baba, ya tattauna da wakilin mu a lokacin da yake aikin Hajji a Saudiyya cewa, rashin yin gaggawar sauya jiragen zai iya jefa rayuwar Shugaban Ƙasa cikin haɗari.

“Kun ga rahoton kwamitin kuwa? Saboda sai da kwamitin ya zurfafa bincike sosai kafin ya fito da rahoton sa. Ya gayyato jami’an da ke kula da bargar jiragen Shugaban Ƙasa ya ji ta bakin su.

“Kwamitin ya samu duk wasu bayanai da yake buƙata, waɗanda haka ɗin ya sa kwamitin ya hanzarta cewa akwai buƙatar gaggawar sayen jirage ga Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa.

“Gaskiya ne mu na fama da matsanancin tattalin arziki, to amma kuma hakan ba zai iya zama dalilin jefa rayuwar shugaban ƙasar mu, mataimakin sa, manyan ƙasa da jami’an kula da jeragen da ma sauran jama’a a cikin haɗari ba.

“Ya kamata abin da ya samu Shugaban Ƙasar Iran da Mataimakin Shugaban Ƙasar Malawi ya zama darasi gare mu.”

A ranar Juma’a dai wannan jaridar ta buga labarin cewa ‘Yan Majalisa na so a gaggauta sai wa Tinubu da Shettima sabbin jirage na zamani.

Kwamitin Majalisar Tarayya masu Lura da Fannin Tsaro da Leƙen Asiri, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sayen sabbin jirage gadagau ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Wannan kira ya zo ne daidai lokacin da ake ta ƙadabolo tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC, TUC da kuma Gwamnatin Tarayya.

Kwamitin ya yi wannan kira a cikin wani rahoto da ya miƙa, bayan wani ƙaramin kwamiti ya gudanar da zaman sauraren irin halin inganci da nagartar da jiragen shugaban ƙasa ke ciki.

“Kwamitin ya gamsu cewa akwai buƙatar gaggawa domin a sayo wa Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa sabbin jirage. Hakan zai kawai da fargaba ko shakkun afkuwar wani abin da ba fatan afkuwar sa ake ba.”

PREMIUM TIMES ta samu rahoton wanda Shugaban Kwamiti, Ahmed Satomi da Magatakardar Majalisa, Makwe Eric suka sa wa hannu.

Wasu ‘yan majalisar sun ce tuni har ma an aika wa Shugaban ƙasa rahoton, domin ya ɗauki matakin da ya dace.

Rahoton dai ya ce akwai jirage shida a bargar jiragen Shugaban Ƙasa. Sai kuma helikwafta guda shida, waɗanda biyu daga cikin su ko an yi masu garambawul ba za su iya cirawa sama ba.

Kwamitin ya ce jirgin da shugaban ƙasa ke hawa ya kai shekaru 19, kuma samfurin Boeing 737 ne, kuma a yanzu haka ya na can ana yi masa garambawul na shekara-shekara.

Shi kuwa na Mataimakin Shugaban Ƙasa, shekarar sa 13, kuma samfurin Gulfstream G550 ne, amma lafiyar sa ƙalau.

People are also reading