Home Back

Ramaphosa: Kafa gwamnatin hadaka abu ne mai kyau

dw.com 2024/7/2
Südafrika Kapstadt | Vereidigung Präsident Cyril Ramaphosa in der Nationalversammlung
Hoto: Nic Bothma/REUTERS

Wannan ne dai karo na farko a tsawon shekaru 30 da jam'iyyar ANC ta Ramaphosa ta kwashe tana mulki, aka samu gwamnatin hadaka tsakaninta da DA din da ta kwashe tsawon wadannan shekaru a matsayin babbar jam'iyyar adawar kasar. Lateefa Mustapha Ja'afar ta hada mana rahoto kan wannan batu.

Gwamnatin hadakar ta Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun da ke zaman irinta ta farko tun bayan komawar kasar kan turbar dimukuradiyya a shekara ta 1994 dai, ta kunshi jam'iyyu biyar ne. Bayan babbar jam'iyyar adawar ta Democratic Alliance DA ta masu tsantsar kishin kasa da ra'ayin jari-hujja, akwai kuma wasu kananan jam'iyyu Inkatha Freedom Party (IFP) ta 'yan kabilar Zulu da Patriotic Alliance (PA) ta masu kyamar baki da kuma 'yar karamar jam'iyyar masu rajin kawo sauyi wato GOOD Party. Jam'iyyar ANC ta nunar da cewa gwamnatin hadakar ta hadin kan kasa, za ta kunshi wakilcin duk jam'iyyun kafin a amince da kuma daukar duk wani mataki a gwamnatin. Da yake jawabi a yayin rantsar da shi a karo na biyun, Shugaba Ramaphosa mai shekaru 71 a duniya ya nunar da cewa:

"Fahimtar cewa babu wata jam'iyya da za ta iya yin mulki da samar da dokoki ita kadai, ya sanya wadannan jam'iyyun suka amince da yin aiki tare su samar da mafita da kuma ci-gaba ga al'ummar Afirka ta Kudu. Sun amince da samar da gwamnatin hadin kan kasa, domin tsara mafita  guda da nufin kawo sauyi mai dore wa. Kafa gwamnatin hadin kan kasa, wani yanayi ne mai muhimmanci. Wannan mafari ne na sabon karni na siyasa."

'Yan majalisar dokokin Afirka ta Kudun sun sake zabar Ramaphosa a matsayin shugaban kasa a Jumma'ar da ta gabata, bayan ya gaza yin nasara karkashin jam'iyyarsa ta ANC a babban zaben da aka gudanar a watan Mayun bana da babu jam'iyyar da ta iya kai bantenta a kasar. A zaben na Mayu ANC din ta sha da kyar da kaso 40 cikin 100, maimakon sama da kaso 57 cikin 100 da ta samu a zaben baya. Sai dai gwamnatin hadin kan kasar ta samu kakkausar suka daga jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin sauyi da kuma ceto tattalin arzikin kasa EFF karkashin jagorancin Julius Malema. Da yake zantawa da manema labarai kan sabuwar gwamnatin ta Afirka ta Kudu, Malema ya ce:

"Zamu kama bangaren gudanarwar da alkawarin da suka dauka, babu wata gwamnatin hadin kan kasa da za mu bari ta yi abin da ta ga dama. Akwai kwakkwarar adawa da za ta sanya musu ido, wannan shi ne abin da za mu yi."

A nata bangaren jam'iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta yi fatali ne da shiga duk wata gwamnati da ta kunshi jam'iyyar masu kyamar baki ta fararen fatar kasar wato PA da kuma ta masu tsantsar kishin kasa da ra'ayin jari hujja DA. Jam'iyyar ta MK da ta zo matsayi na uku a zaben da ya gabata karkashin Zuma ta sha alwashin hada kai da kananan jam'iyyu a majalisar dokokin kasar, domin yakar gwamnatin karkashin jagorancin ANC da DA. A yayin wani taron manema labarai kwanaki kalilan gabanin sake rantsar da Ramaphosa a matsayin shugaban kasa, Zuma ya bayyana cewa:

"Sun yanke shawarar sanya kasarmu cikin yaki. Sai yanzu suke sanar da cewa ya kamata mu hada kanmu mu kafa gwamnatin hadin kan kasa, wannan ba abu ne mai ma'ana ba domin ba su ce komai ba."

Manyan baki da suka halarci bikin sake rantsar da Ramaphosa a matsayin shugaban kasar Afirka ta Kudu sun hada da shugabanni daga Kuba, da shugabannin kasashen Afirka da suka hadar da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da Joao Lourenco na Angola da na Kongo Brazzaville Denis Sassou Nguesso da kuma na Eswatini Sarki Mswati na III. Ana kuma sa ran Ramaphosa ya sanar da majalisar ministocinsa nan da kwanaki kalilan, a daidai lokacin da suke ci gaba da tattaunawa da mambobin gwamnatin hadakar.

People are also reading