Home Back

Yadda muka fallasa ma’aikatan bogin da ke karɓar albashi a Najeriya, alhali su na can su na wani aikin a ƙasashen waje – Shugabar Ma’aikata

premiumtimesng.com 2024/7/2
Yadda muka fallasa ma’aikatan bogin da ke karɓar albashi a Najeriya, alhali su na can su na wani aikin a ƙasashen waje – Shugabar Ma’aikata

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan, ta bayyana cewa ofishin ta ya bankaɗo ɗimbin ‘yan Najeriya da suka tsallake aikin gwamnatin tarayya, ko kuma dama can ma’aikatan bogi ne masu karɓar albashi, su na zaune ƙasashen waje kuma su na wani aikin a can.

Folasade ta bayyana haka a taron manema labarai, ranar Laraba. Taron dai na daga cikin shirye-shiryen Makon Ma’aikata na 2024 a Najeriya.

Ta ce tun da farko kwanan baya ne dai “na yi sanarwa aka tura kowace ma’aikata, cibiyoyi da hukumomi cewa za a yi tantancewar ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato ta ido-da-ido, wadda tilas duk wani mai karɓar albashi ana so ya bayyana domin a tantance shi.

“A cikin sanarwar na gargaɗi kowane Babban Sakatare da Shugaban Hukuma ko na Cibiya cewa idan aka cusa bayanai na ƙarya ko aka kawo min lissafin-dawakan Rano, to su kuka da kan su.

“Mun fito da wannan tsari domin mu gano masu karɓar albashi alhali sun bar aiki, amma ba su zo an saka sunayen su a jerin waɗanda ba su yi ritaya ba.” Cewar ta.

Folasade ta ce wannan tantancewa na daga cikin nasarorin da ta samar, domin ya daƙile ɗimbin masu karɓar kuɗaɗe alhali ba ma’aikatan gwamnatin tarayya ba ne.

“Abin mamaki, wasu ma fa daga Ingila suka riƙa garzayowa Najeriya su na zuwa domin a tantance su. Haka wani shugaban wata ma’aikata ya faɗa min, yayin da na ga sunayen waɗanda ba a tantance ba sun ma fi na waɗanda aka tantance yawa.

“Na tambaye shi ya me ya sa aka yi haka?
Sai ya ce min ai ba mu tantance su ba. Duk wanda ya zo ya ce oga, ka san ni maaikaci ne fa har yanzu, sai na ce to ka je ka dawo nan da mako biyu a tantance ka. Na yi masu haka ne domin na san a Ingila ba za taɓa barin wani mai aiki ya zo Najeriya har ya yi mako biyu ba.”

Ta ce tsarin tantance ma’aikata ido na ganin ido ya rage karkatar da maƙudan kuɗaɗe, kuma ya samar da sauƙin tafiyar da aikin gwamnati a sauƙaƙe.

People are also reading