Home Back

Da sojoji ake haɗa baki ake satar ɗanyen man Najeriya – Jami’in IPMAN

premiumtimesng.com 4 days ago
Soldiers in the forest
Soldiers in the forest

Babban Kodinetan Ƙungiyar Manyan Dillalan Fetur na Najeriya (IPMAN), ya yi zargin cewa da haɗin bakin jami’an tsaron Najeriya ake ɗibga satar ɗanyen mai a kasar nan, can a yankin Neja Delta.

Ya bayyana haka a wata tattaunawa da shi da aka yi a gidan talabijin na Arise TV.

Musa Saidu ya ce duk da irin hanyoyin daƙile yawan satar tulin ɗanyen mai da NNPC ya shigo da su, amma abin baƙin ciki wasu jami’an tsaro na yi masu ƙafar ungulu ta hanyar haɗa baki da ɓarayin ɗanyen mai ana sakin jiragen ruwan da akan kama da lodin ɗanyen mai na sata.

“NNPC na bakin ƙoƙarin ta wajen ganin an daƙile matsalar ɓarayin ɗanyen mai, amma wasu jami’an tsaro ko an kama jiragen ruwa ɗauke da ɗanyen mai sai su sa a sake su,” inji shi.

Ya ce duk da rahoton da suka damƙa wa gwamnatin tarayya, jami’an tsaro sun ƙi yin komai a kai.

Ya ce rahoton na ɗauke sunayen masu hannu dumu-dumu a harkar satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta.

Daga nan ya buga misali da yadda suka fallasa wani jirgi mai ɗauke da ɗanyen mai na sata, har sojoji suka kama shi, amma daga baya wani babban soja ya sa aka saki jirgin ruwan.

Ya ce sun bi sawu su na ƙorafi har Ma’aikatar Tsaro ta Ƙasa, amma maganar kenan.

Ya ce su da NNPC ba su da bindigogi, babu abin da za su iya.

Sai dai kuma Sojojin Najeriya sun ƙaryata wannan zargi da ya yi masu, kamar yadda Kakakin Sojojin Saman Najeriya, Edward Gwabkwet ya yi wa PREMIUM TIMES bayani.

People are also reading