Home Back

Matsalar Nijeriya Ba Daga APC Ba Ce – Gwamna Uzodimma

leadership.ng 2024/8/23
APC

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta APC ta yi iya bakin kokarinta wajen ciyar da kasar nan. Ya ce kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar nan duka a duniya ne.

Uzodimma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC (PGF), ya bayyana haka a Abuja lokacin da ya jagoranci zababbun gwamnonin jam’iyyar APC a ziyarar da suka kai wa shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda yake jagorantar kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyya mai mulki.

Gwamnan ya ce, “Gaskiyar magana ita ce, jam’iyyar APC ta yi kokari sosai a Nijeriya. Abin da ke faruwa a halin yanzu matsalar ce na tattalin arzikin duniya baki daya.

“Mu a Nijeriya karkashin jagorancinmu na Shugaban kasa, Bola Tinubu mun fitar da tsare-tsare don magance matsin tattalin arziki, idan aka yi la’akari da irin tattalin arzikin da yake ciki duba da irin yanayin da ya samu kansa. Ina da yakinin cewa nan ba da dadewa ba ‘yan Nijeriya za su dara.”

Dangane da damar da jam’iyyar take da shi na samun nasara a zaben gwamnonin Edo da Ondo duba da halin kuncin da kasar nan ke ciki, Uzodimma ya ce jam’iyyar APC ce ke rike da jihohi 20 cikin 30 na kasar nan, tare da shugabancin kasa, kuma idan har zabe abu ne wanda yake tattare da wayan jama’a, lallai masu rinjaye ne za su samu shugabanci.

A nasa bangaren, Ganduje ya ce shugabannin jam’iyyar za su yi kokarin kulla kyakkyawar alaka da gwamnoni a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Ya ce, “Babu shakka mun yi matukar farin ciki a yau da na samu labarin kuna zuwa. Don haka, ina ganin wannan wata ni’ima ce mai girma a gare mu. Saboda haka, mun yi farin ciki da wannan ziyara kuma muna da kwarin gwiwa a kanku.

“Za mu yi duk mai yiwuwa don ganin mun ci gaba da wanzar da kyautata alaka da gwamnoninmu a fadin kasar nan, kuma za mu taimaka wajen kare muradunsu wanda ko shakka babu su ma suna taimaka wa jam’iyyar, suna sa jam’iyyar ta yi kara armashi kamar yadda ya kamata.”

Uzodinma ya kasance tare da Gwamnan Jihar Kuros Riba, Bassey Out da Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa da takwaransu na Jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji a wurin wannan ziyara

People are also reading