Home Back

Malaman Sakandire ku guji karɓar kuɗi a wajen iyayen yaran da za suyi rijistar NECO – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/7/4

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi dukkanin shugabannin makarantun sakandaren jihar, kan su guji karɓar kuɗi a hannun iyayen yara, idan sun zo yin rijistar jarrabawar NECO.

Shugaban hukumar da ke kula da manyan makarantun sakandaren jihar Kano Dakta Kabiru Ado Zakirai, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawar sa da manema labarai ranar Juma’a, a ofishin sa da ke Kano.

Ya kuma ce gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya ɗauki aniyyar biya wa duk ɗalibin da ya samu nasarar samun maki huɗu, wato (Four Credit) a jarrabawar Qualifying, ba tare da la’akari da ɗalibi ya ci darasin Turanci ko lissafi ba.

A cewar sa, “Ya zama wajibi kowanne ɗalibi ya hanzarta zuwa makarantar sa domin yin rijistar jarrabawar ta (NECO) domin gudun samun matsala, “in ji shi”.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa Dakta Kabiru Ado Zakirai, ya kuma ja hankalin waɗanda za su yiwa ɗaliban rijista da su kula ka da a samu matsala wajan cike takardun musamman ma a fagen cike shekarun haihuwar su.

People are also reading