Home Back

An haramta duk wani Film dake nuna harkar Daba ko Daudu a Kano

dalafmkano.com 2024/5/19

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jihar Kano, ta haramta duk wani shirin fin da ta kunshi Daba, ko Daudu a fadi jihar Kano.

Shugaban hukumar tace fina-finan ta Jihar Kano Abba Al-Mustapha, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai a yau Laraba, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bisa yadda hakan ya ke koyar da harkar Daba, wanda ya saɓa da addinin Musulunci da kuma al’adar Bahaushe.

“Ba zamu ƙara sahale ko tace duk wani shirin Film ɗin Hausa da akayi harkar Daba, ko Daudu ba a cikin sa domin doka ta dakatar da haska shi, “in ji shi”.

Al-Mustapha, ya ƙara da cewa sun kuma bai wa masu shirya fina-finai wa’adin wata ɗaya da duk wani fin da ya shafi amfani da makami ko Daudu domin a tantance shi kafin shigar sa kasuwa, kamar yadda wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito.

People are also reading