Home Back

ECOWAS ta ja hankalin kasashen AES kan ficewa daga kungiyar

dw.com 2024/5/19
Ghana Symbolbild ECOWAS Fahnen
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Majalisar dattijan ECOWAS ko kuma CEDEAO ta kammala taron kwanaki biyu a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire kan rayuwar kungiyar da kuma dambarwar da ake fama da ita a yankin yammacin Afrika. 

A cikin sanarwar ta biyo bayan taron shugaban majalisar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonatan ya bayyana damuwa a game da matakin kasashen yankin Sahel uku da ke karkashin mulkin sojoji da suka hadar da Burkina Faso da Nijar da Mali na raba gari da kungiyar.

Kazalika majalisar dattijan ta tabo batun katsalandan da wasu manyan kasashe ke yi a yankin yammacin Afrika, da kuma raunin kasashen kungiyar, tare da yin kira ga hukumar gudanarwar ECOWAS da ta dauki matakin gaggawa don hana yankin zama fagen yada rikice-rikice kan manufofin siyasa na kasa da kasa.

Kasashen uku da ke yankin Sahel dai sun kafa wata kungiya da ake wa lakabi da AES tare da kulla alaka da Rasha bayan korar sojojin Faransa da ke zama uwar gijiyarsu a shekarun baya. 

People are also reading