Home Back

Dangote Ya Ci Gyaran Gwamnatin Tinubu, Ya Ce CBN Ya Kawo Tsarin Ruguza Sana’o’i

legit.ng 2024/7/3
  • Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce akwai gyara a kan yadda gwamnatin Bola Tinubu ta kara kudin ruwa
  • Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa tsarin bai dace da kasa kamar Najeriya da ake kokarin samar da ayyukan yi ga al'umma ba
  • Har ila yau, Alhaji Aliko Dangote ya koka kan yadda Najeriya ke kara dukufa wajen shigo da kayayyaki daga ƙasashen ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote ya ja hankalin gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan kara kudin ruwa zuwa kashi 30%.

Aliko Dangote ya ce yin hakan zai kara durkusa sana'o'i tare da rufe kofa ga waɗanda suke ƙoƙarin fara sana'a.

Aliko Dangote
Dangote ya yi magana kan karin kudin ruwa. Hoto: Dangote Foundation Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dangote ya yi bayanin ne a yau Talata yayin taron kungiyar MAN a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote a kan karin kudin ruwa ga sana'o'i

Alhaji Aliko Dangote ya ce karin kudin ruwa ga masu karbar rance zai hana yan kasuwa da dama zama da kafafunsu.

Dangote ya kara da cewa ba lallai a iya samar da sana'o'i da matasa ba matukar kudin ruwa ya karu sosai, rahoton Channels Television.

Har ila yau, attajirin ya ce hatta kamfanoni ba za su tsira daga shiga cikin matsalar durƙushewa ba idan aka samu karin kudin ruwa ya yi yawa.

Aliko Dangote ya bukaci gwamnati ta sassauta

Aliko Dangote ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sassauta kuɗin ruwan domin ceto sana'o'i daga rushewa.

Ya ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta dubi yadda ƙasashen yamma suka kawo tsare-tsaren da za su tallafawa kananan sana'o'i da kamfanoni.

Dangote: 'Mu nisanci shigo da kayan waje'

Aliko Dangote ya yi kira ga yan Najeriya kan rage shigo da kayan amfanin yau da kullum daga ƙasashen ketare.

Ya ce hakan tamkar mutane na gayyato talauci ga kansu ne domin suna gina wasu ƙasashe maimakon gina kasarsu.

Motoci: Dangote zai dawo aiki da gas

A wani rahoton, kun ji cewa a kokarinsa na taimakawa Bola Tinubu wurin rage dogaro da man fetur, Aliko Dangote zai koma motoci masu amfani da gas.

Dangote ya sanar da cewa zuwa shekarar 2025, dukkan motocinsa da ke kamfanin siminti za su koma amfani da gas madadin dizil da fetur.

Asali: Legit.ng

People are also reading