Home Back

Bola Tinubu Ya Yi Magana Kan Faɗuwar da Ya Yi a Filin Faretin Sojoji, Ya Faɗi Gaskiya

legit.ng 2024/6/29
  • Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a karon farko kan zamewar da ya yi ya faɗi a lokacin hawa motar fareti a birnin tarayya Abuja
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa shi ɗan yarbawa ne kuma ya ɗan taɓa wasan al'adar da ake kira dobale domin murnar ranar dimokuraɗiyya
  • Faɗuwar Tinubu yayin da zai hau motar da za ta zagaya da shi ya kalli faretin sojoji a Eagle Square ta haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zamewar da ya yi har ya faɗi ƙasa a lokacin da zai hau mota a filin Eagle Square ranar Laraba.

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda Tinubu ya zame a lokacin da yake ƙoƙarin hawa motar faretin bikin ranar dimokuraɗiyya.

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya ce faɗuwar da ya yi ba wani abin damuwa ba ne domin duk cikin murna ne Hoto: @NGRPresident Asali: Twitter

Bayan faruwar lamarin, kafafen sada zumunta suka hargitse da mayar da martani, inda mutane suka riƙa tofa albarkacin bakinsu kan faɗuwar Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake tsokaci kan lamarin a wurin liyafar cin abinci da aka shirya, Shugaba Tinubu ya ayyana faɗuwar a matsayin wani salon suwaga, Daily Trust ta ruwaito.

Bola Tinubu ya kira zamewar da ya yi a matsayin salon takama, wanda ya rikita kafefen sada zumunta.

"Da safiyar yau, na gamu da wani tsautsayi kuma nan take ya mamaye soshiyal midiya, sun rikice sun gaza gane ko 'buga' na yi ko 'babbaringa'.

"Amma ku tuna ranar ce ta murnar dimokuraɗiyya wadda muna wasan Dobale a wannan rana. Ni ɗan yarbawa ne saboda haka na ɗan taɓa nawa wasan dobale nw kawai."

Tun farko dai fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani kan abin da ya faru, inda ta bayyana cewa Bola Tinubu mutum ne kamar kowa da tsautsayi ka iya afka masa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya jajantawa Tinubu sakamakon faɗuwar ya yi a wurin faretin sojoji na ranar dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

People are also reading