Home Back

Kotu Ta Hana Tsawaita Belin DCP Abba Kyari

leadership.ng 2024/7/1
Kotu Ta Hana Tsawaita Belin DCP Abba Kyari

A yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi bayar da belin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da aka dakatar.

Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin cewa bayar da belin yana bisa ga hurumin kotu ne, kamar yadda sashi na 161 (2) na hukumar kula da shari’a ta (ACJA) ya tanada. Ya bayyana cewa wanda ake tuhumar bai bayar da isassun shaidun da za su tabbatar da beli ba.

Alkalin ya bayyana cewa, ana bayar da beli ne galibi idan laifukan da ake zargin sun kai hukuncin daurin shekaru biyu, yayin da a shari’ar Kyari, hukuncin daurin shekaru 25 ne.

A baya dai, a ranar 22 ga watan Mayu, alkalin ya bayar da belin Abba Kyari na mako biyu, domin ba shi damar kammala jana’izar mahaifiyarsa, wanda daga baya aka tsawaita da mako guda.

Abba Kyari ya cika sharuddan belin kuma an sake shi a ranar 1 ga watan Yuni. Sai dai yayin zaman na yau, Mai shari’a Nwite ya ƙi ƙara tsawaita belin amma ya amince da ƙara sauraran ƙarar.

People are also reading