“Dalili 1 da Ya Sa NLC Ke Zuzuta Albashin Ƴan Majalisun Tarayya”, in Ji Hon. Rotimi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce kungiyoyin kwadago suna yada "labarai marasa tushe" game da albashin 'yan majalisar dokokin kasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Rotimi ya kuma caccaki 'yan kwadagon kan rufe muhimman ma'aikatu yayin yajin aikin da suka yi a fadin kasar a ranar Litinin.
Mai magana da yawun majalisar ya ce majalisar wakilai na "goyon baya" ga kiran da ake yi na inganta albashi da yanayin aiki ga ma'aikata, in ji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya gargadi cewa:
"Akwai bukatar yin taka tsan-tsan wajen kara mafi karancin albashi. Idan ya zarce karfin tattalin arzikinmu to zai jawo hauhawar farashin kayayyaki, korar ma'aikata daga aiki, da sauran illolin tattalin arziki."
"Don haka, akwai bukatar mu tunkari wannan batu ta hanya madaidaiciya domin tabbatar da ma'aikata, gwamnati da tattalin arziki ba su takura ba na dogon lokaci."
Jaridar Vanguard ta ruaito sanarwar mai magana da yawun majalisar wakilan ta ci gaba da cewa:
“Hakazalika, alkiblar yajin aikin da 'yan kwadagon suka shiga kafin dakatar da shi ya jefa mu a damuwa, saboda akwai babban kalubalen da ka iya haifarwa a gaba.
“Rufe muhimman ma'aikatu, kamar tashar wutar lantarki ta kasa, ya zama zagon kasa ga tattalin arziki kuma yana da illa ga rayuwar kasarmu da jama'ar ta."
Hon. Akin Rotimi ya ce yana da mahimmanci a magance jita-jitar da shugabannin ƙwadago ke yadawa game da albashin 'yan majalisu.
“'Yan kwadago sun kwashe shekaru suna yada labaran karya game da albashin ‘yan majalisun tarayya, duk domin su harzuka jama’a da kuma zubar da mutuncin majalisar.
“Wannan karairayin na karkatar da hankalin jama'a daga muhimman batutuwan da ke faruwa da kuma cin mutuncin majalisar, wanda ya kamata 'yan kwadago su daina."
- In ji Rotimi.
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin bayan ganawarsu da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.
A yayin ganawar, shugabannin kwadago da wakilan gwamnatin sun cimma matsaya kan abin da ya shafi mafi karancin albashin ma'aikatan kasar.
Asali: Legit.ng