Home Back

Amurka ta bai wa Ukraine tallafin manyan kayan yaƙi

bbc.com 2024/5/10
...

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Amurka ta bayar da bayanin tallafin soji na dala biliyan shida da ta bai wa Ukriane, wanda ya mayar da hankali ga samar da tsaro ta samaniya.

Wannan ne karo na biyu da Amurkan ke fitar da maƙudan kuɗi domin tallafawa Ukraine, bayan amincewa da ƙudirin yin hakan a Washington, a farkon mako.

Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin, ya ce kayan yaƙin da za a saya da kuɗin sun haɗa da na’urar kariya daga harin makami mai linzami, da na’urar kakkaɓo jiragen yaƙi da kuma manyan tankokin yaƙi.

A yayin wata ganawa da, manema labarai a hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon, Mr Austin ya ce tallafin zai mayar da hankali ne wajen bai wa Ukarine damar ƙarfafa tsarin kare kai daga harin makami mai linzami da kuma bnƙasa ƙarfin ta a yaƙin.

Ya ce: "Ina jan hankalin mu a kan kaucewa mayar da hankali ga samar da na’urar kare harin makami mai linzamin ita kaɗai. Ina ganin kamata ya yi shirin ya zama na samar da ingattaccen tsarin tsaro na sama da kuma na ƙasa. Akwai kuma ƙarin abubuwan da suke buƙata da muke fatan ganin sun samu. Wataƙil mu iya kai wa ga Ukraine cikin gaggawa, amma wannan aiki ne da zia ci gaba da gudana."

Ba a dai yi tanadin bayar da sabuwar na’urar kakkaɓo harin makami mai linzami ta sama ba.

Amma Amurka na fatan tallafin zai taimakawa Ukraine wajen bunƙasa tsaron ƙasar ta.

People are also reading