Home Back

TSANANIN ZAFIN RANA: Mazauna Kano, Abuja, Sokoto da Kogi su yi kaffa-kaffa da samun bugun zuciya – NiMet

premiumtimesng.com 2024/5/6
TSANANIN ZAFIN RANA: Mazauna Kano, Abuja, Sokoto da Kogi su yi kaffa-kaffa da samun bugun zuciya – NiMet

Hukumar NiMet ta yi gargaɗin cewa mazauna jihohin Kano, Abuja, Sokoto da Kwara su yi hattara, domin tsananin zafin da ake fama da shi ka iya haifar masu da bugun-zuciya.

Ciwon bugun zuciya dai ciwo ne mai kaiwa ga kisa, wato ya na afkuwa idan mutum ya kasance tsananin zafi ya galabaitar da shi.

NiMet ta ce a ranar Alhamis mazauna waɗannan jihohi za su jigata sosai saboda tsananin zafi, wanda zai iya haddasa masu matsalolin da zafi ke haddasawa.

Cikin wata takardar gargaɗi da kuma shawarwari, tare da rarrabe jihohi 36 da Abuja gwargwadon tsananin zafin da za su fuskanta.

Akwai zafi maras illa, sai Zafi Mai Takurawa, sai Zafi Mai Tsanani, Zafi Mai Hatsari. Wannan kuma ya danganta ne da irin gejin zafin kowane yanki.

“Tsananin zafi zai addabi jama’a a wasu jihohi. Ya zama wajibi mu gargaɗi mutane su ɗauki matakan gaggawa,” inji NiMET.

An lissafa Abuja, Kano, Sokoto da Kogi ne za su fuskanci tsananin zafi. Don haka ake gargaɗin mazauna jihohin su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki, saboda zafin zai iya haddasa masu cutar bugun zuciya.”

Akwai kuma wasu jihohi da ke cikin wannan rukunin, waɗanda suka haɗa da Kebbi, Katsina, Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Neja, Zamfara, Nasarawa, Jigawa, Benuwai da kuma Kwara.

People are also reading