Home Back

Na janye kalaman ɓata wa A-A Zaura suna a Kotu – Likita

dalafmkano.com 2024/7/6

Kotun majistrert mai lamba 51 karkashin mai Shari’a Ibrahim Mansur Yola, ta sanya ranar 25 ga wannan watan domin bayyana matsayarta a kan tuhumar da ƴan sanda ke yiwa Dakta Sulaiman Musa Ɗan Takarda da laifin ɓata suna.

Tun da fari dai ƙunshin zargin da a ke yi wa Dakta Sulaiman Musa ya bayyana cewar, a ranar 22 ga watan 2 na wannan shekara Sulaiman ya ɓata wa Abdulkarim Abdussalam, A-A Zaura suna, ta hanyar yaɗa wasu maganganu a shafinsa na Facebook, inda ya kira shi da Ɗan Damfara.

A zaman kotun na yau mai kara A-A Zaura ta bakin wakilinsa Alhaji Ado Zaura, sun bayyana cewar sun janye ƙarar da suke akan wannan matashi.

Wakilinmu na Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa yayin zaman kotun, matashin ya janye kalamansa har ma ya ce sharrin shaiɗan ne kuma ba zai sake ɓata sunan wani ba.

People are also reading