Home Back

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka da Yawa a Arewa

legit.ng 2024/7/1
  • Ƴan bindiga sun kai mummunan hari garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun kashe bayin Allah
  • Mazauna garin sun bayyana cewa yawan ƴan bindigar ya sa babu jami'in tsaron da ya iya tunkararsu, sun kuma tafi da mutane 50
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce tuni suka fara gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Adadi mai yawa na ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun tarwatsa garin Maidabino, gari na uku mafi girma a ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina.

Maharan sun kashe kusan mutane tara a harin, kuma sun yi garkuwa da wasu mutum 50 waɗanda galibi mata ne da ƙananan yara.

Gwamna Malam Dikko Radda.
'Yan bindiga sun halaka mutane da dama a garin Maidabino da ke Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Asali: Facebook

Wani mazaunin Maidabino ya tabbatarwa Daily Trust cewa ƴan bindigar sun ɗauke sa'o'i suna cin karensu babu babbaka ba tare da an tanka masu ba saboda yawansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sama da gidaje 10 da shaguna 15 da motoci akalla tara ne ‘yan ta’addan suka kona a mummunan harin na ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi.

Mutumin ya ce ƴan bindigar sun shiga garin tun karfe 10:00 na daren ranar Asabar har zuwa karfe 2:30 na dare.

"Abin da ya faru tun farko shi ne, ranar Jumu'a, sojoji sun rako kusan motoci 30 na ƴan Kasuwa da suka dawo daga kasuwar Ƴantumaki, kwatsam suka ci karo da ƴan bindiga a titin zuwa Maidabino.
"Sojojin sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindigar a musayar wuta, hakan ya sa suka koma suka haɗa ƴan uwansu ƴan bindiga da yawa ta yadda sojojin ba za su iya tunkarar su ba.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Kakakin ƴan sandan ya ce mutum 7 aka kashe a harin kuma yanzu haka jami'an tsaro sun fara bincike kan lamarin.

Kuna da labarin cewa Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da kai samame kan ƴan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar nan.

Hedkwatar tsaro (DHQ) ta ce sakamakon haka sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 220, sun kamo wasu 395 tare da ceto mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

People are also reading