Home Back

DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta goyi bayan Sarki Muhammadu Sanusi II

premiumtimesng.com 2024/7/3
SANUSI YA DAWO: Gwamna Abba Yusuf ya maida Muhammadu Sanusi II Gidan Dabo

Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), ta bayyana goyon bayan ta ga halascin naɗa Sarki Muhammadu II a Kano, bayan rushe masarautu biyar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi.

A taron da NBA ke gudanarwa na ƙasa yanzu haka a Kano, Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wani babban taro da ta gudanar a jihar. An yi taron ne a yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, NBA ta amince da Sanusi II a matsayin halaltaccen Sarkin Masarautar Kano guda ɗaya.

Baya ga wakilcin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya tura Walin Kano, Mahe Bashir Wali, taron ya kuma samu halarta daga Shugaban Kotun ‘National Industrial Court’, Mai Shari’a Benedict Bakwaph-Kanyip, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), Yakubu Maikyau da kuma Cif Jojin Jihar Kano, Dije Aboki, da sauran manyan masana harkokin shari’a.

Sarkin Kano Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron, ya ce har sai akwai ƙarfin shari’a a ƙasa ne al’umma ke iya yin rayuwa cikin salama.

Jaridar THE NATION da wasu jaridu da dama sun ruwaito cewa wannan amincewar na zuwa bayan da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano da hakiman su, kwamishinoni da wasu manyan jihar suka yi mubaya’a ga sabon sarkin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Ƙungiyar NBA ta amince da naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II ne bayan ta gayyace shi taron ta na shekara da ke gudana yanzu a Kano.

La’akari da girman wannan taron, ƙungiyar lauyoyin ta gayyaci Sarkin Kano na 16, domin ya gabatar da jawabin sanya albarka a matsayin sa na uban ƙasa.
An ce ƙungiyar ta NBA ba ta gayyaci Alhaji Aminu Ado Bayero ba, wanda dokar masarautar Kano ta 2024 ta tsige shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 15.

A rannar Litinin ce dai Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta shirya sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan rigimar masarautar, amma saboda yajin aikin NLC ba ta samu zama ba.

Sarki Muhammadu Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron NBA, ta bakin wakilin sa, Walin Kano, Mahe Bashir Wali, ya yi wa baƙi maraba da nuna girman al’adun Jihar Kano. Sarkin ya ce har sai akwai ƙarfin shari’a a ƙasa ne al’umma ke iya yin rayuwa cikin salama, wanda kuma ya ce bunƙasar al’umma na tattare da ƙarfin shari’a.

Gwamnan Kano Ya Ƙalubalanci Lauyoyi:

A ɓangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kuwa, ya yi amfani da damar taron wajen ƙalubalantar NBA kan makomar umarnin kotuna biyu game da rigimar masarautar jihar. Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Bappa Bichi ya nemi lauyoyin da su riƙa wayar da kan abokan hulɗar su kan hurumin kotuna a shari’a. Abba Yusuf ya ce akwai kotun da ba ta da hurumin sauraron shari’ar rigimar Masarautar Kano, kasancewar rigima ce ta cikin gida, wadda kotun jiha ke da hurumin saurare.

Da yake zantawa da manema labarai kan rikicin Masarautar Kano, Barista O.M Femi ya ce ƙungiyar NBA ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa. Barista O.M Femi ya ce: “Duk da haka, ba ka buƙatar a gaya maka ko ka sanya tabarau kafin ka san cewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano na 16 a yanzu.

“Haka zalika, gayyatar Sarki Muhammadu Sanusi II zuwa wannan babban taron na NBA zai ƙara ba ka tabbaci na wanda muke kallo a matsayin Sarkin Kano na 16.” Cewar sa.

Yayin da aka dakatar da yajin aiki, yanzu kuma hankula sun karkata domin jin ranar ta za a koma kotu, dangane da rigimar masarautar.

People are also reading