Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Manyan Hadimai 3 Daga Aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta dakatar da wasu manyan jami'anta guda uku.
Hukumar kula da ma'aikatan jihar Bauchi ce ta dakatar da manyan jami'an bisa zargin amfani da takardun bogi da kuma almundahana.
Rahoton Leadership ya tattaro cewa waɗanda aka dakatar sun haɗa da babban Akanta na ma'aikatar lafiya, Yakubu Muhammad.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sune babban jami’in gudanarwa na sashin baitul-malin Bauchi, Surajo Shehu Ilela, da mataimakin jami’in Gudanarwa na hukumar harkokin sadarwa, Umar Muhammad Misau.
Tuni dai gwamnatin Bauchi ta janye naɗin da aka yiwa Umar Misau, har sai an kammala bincike kan zarge-zargen da ke kansa.
An tattaro cewa laifukan da ake zargin jami'an uku da aikatawa sun sabawa tanadin dokokin aikin gwamnati mai lamba 0327 (a) da (b) bi da bi.
Jami’in yada labarai na hukumar kula da ma’aikata ta jihar Bauchi, Saleh Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi ranar Laraba.
Ya ce an tattauna batun dakatarwar kuma an amince da shi a wurin babban zaman hukumar da ya gudana karo na 21.
A daya bangaren kuma, Umar ya ce hukumar ta kuma duba tare da amincewa da nadin sababbin daraktoci hudu da mataimakan daraktoci biyu na rikon kwarya.
A wani rahoton kun ji cewa Dokta Goodluck Ebele Jonathan ya zargi wasu gwamnonin jihohi da amfani da ƴan daba wajen maguɗin zaɓe don cimma burinsu na siyasa
Tsohon shugaban ƙasar ya ce maimakon gwamnoni su gina matasan ta hanyar da gwamnati za ta amfana da su, sun zaɓi mayar da su ɓata gari.
Asali: Legit.ng