Home Back

Ganduje Ya Ga Ta Kansa, Wasu Manyan Jiga-Jigai da Mambobin APC Sun Koma PDP

legit.ng 6 days ago
  • Yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar Ondo, wasu jiga-jigai da mambobin APC sama da 1000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa PDP
  • Masu sauya ahekar sun bayyana cewa sun baro APC ne saboda rigingimun cikin gida za kuma burinsa na kawar da jam'iyyar da ta kawo yunwa
  • Sun kuma sha alwashin cewa za su marawa ɗan takarar gwamna a inuwar PDP baya a zaɓen da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Mamban All Progressives Congress (APC) fiye da 1000 a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu sun sauya sheƙa zuwa PDP jihar Ondo.

Masu sauya sheƙar karkashin jagorancin Mayowa Ajemoju Boboye sun bayyana rashin bai wa kowa haƙƙinsa a matsayin dalilin barin APC mai mulki.

Umar Damagun da Ganduje.
PDP ta samu ƙarin goyon baya yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar Ondo Hoto: Umar Damagum, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 8, Deborah Owosusi da Ademola Ayonijebul, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran jiga-jigan da ke cikin tawagar masu sauya shekar sun haɗa Mayowa Boboye, Oloro Alejo, da Azeez Ibrahim wanda ya jagoranci tawagar ƴan Ebira.

Sun yi alkawarin goyon bayan PDP da dan takararta na gwamna Hon Agboola Ajayi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

A cewarsu za su yi duk mai yiwuwa wajen kawar da jam’iyya mai mulki daga gidan gwamnatin Ondo a zaɓe mai zuwa.

Jam'iyyar PDP ta tarbi tsoffin mambobin jam’iyyar APC ne a wani taro da aka gudanar a babban dakin taro da ke birnin Akure.

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya sheka, tsohon sakataren APC a Akure ta Kudu, Akinwande Fayinminu, ya soki shugabannin APC, inda ya zarge su da kawo yunwa a ƙasa.

"APC ta rasa zaman lafiya da adalci a cikin gida shiyasa kuka ga kawunansu sun rabu, ba za mu iya zama a ciki ba," in ji shi.

Fubara ya ɗora laifi kan mutanen Wike

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya zargi mutanen Wike da hannu a kokarin tashin bam a birnin Fatakwal.

Fubara ya bayyana cewa an shirya tayar da bam ne domin a jawo hankalin gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a Ribas.

Asali: Legit.ng

People are also reading