Ganduje Ya Ga Ta Kansa, Wasu Manyan Jiga-Jigai da Mambobin APC Sun Koma PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Mamban All Progressives Congress (APC) fiye da 1000 a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu sun sauya sheƙa zuwa PDP jihar Ondo.
Masu sauya sheƙar karkashin jagorancin Mayowa Ajemoju Boboye sun bayyana rashin bai wa kowa haƙƙinsa a matsayin dalilin barin APC mai mulki.
Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 8, Deborah Owosusi da Ademola Ayonijebul, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jiga-jigan da ke cikin tawagar masu sauya shekar sun haɗa Mayowa Boboye, Oloro Alejo, da Azeez Ibrahim wanda ya jagoranci tawagar ƴan Ebira.
Sun yi alkawarin goyon bayan PDP da dan takararta na gwamna Hon Agboola Ajayi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
A cewarsu za su yi duk mai yiwuwa wajen kawar da jam’iyya mai mulki daga gidan gwamnatin Ondo a zaɓe mai zuwa.
Jam'iyyar PDP ta tarbi tsoffin mambobin jam’iyyar APC ne a wani taro da aka gudanar a babban dakin taro da ke birnin Akure.
Da yake magana a madadin wadanda suka sauya sheka, tsohon sakataren APC a Akure ta Kudu, Akinwande Fayinminu, ya soki shugabannin APC, inda ya zarge su da kawo yunwa a ƙasa.
"APC ta rasa zaman lafiya da adalci a cikin gida shiyasa kuka ga kawunansu sun rabu, ba za mu iya zama a ciki ba," in ji shi.
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya zargi mutanen Wike da hannu a kokarin tashin bam a birnin Fatakwal.
Fubara ya bayyana cewa an shirya tayar da bam ne domin a jawo hankalin gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a Ribas.
Asali: Legit.ng