Home Back

MUGUN FARASHI DA MUGUN TAYI: Ƙaramin albashin Naira 494,000 da NLC ke buƙata zai sa kamfanoni su kori ɗimbin ma’aikata – Akpabio

premiumtimesng.com 2024/6/26
JUYIN MULKI: Sanatocin Najeriya sun ki amincewa da bukatar Tinubu na a tura sojoji don murkushe sojojin juyin mulki a Nijar

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ƙaramin albashi har Naira 494,000 da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, NLC ke buƙata daga gwamnatin tarayya, haddasa kamfanoni masu zaman kan su korar tulin ma’aikata, kuma zai haddasa ambaliyar marasa aikin yi a faɗin ƙasar nan.

“Saboda idan gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin albashi, to za ta mu zuba ido su ma kamfanoni masu zaman kan su bi yi aiki da tsarin. Idan suka kasa ɗaukar nauyin ƙarin albashin kuwa, to abin da zai biyo baya shi ne sallamar ma’aikata birjik.”

Akpabio ya bayyana haka yayin da yake jawabi wurin buɗe taron gaggawa da ya gudana tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da kuma Majalisar Dattawa da ta Tarayya, a Majalisa da ke Abuja, a ranar Lahadi.

An yi taron ne kafin tafiya yajin aiki, kuma taron bai cimma matsaya ba, domin ƙungiyoyin biyu na ƙwadago sun yanke hukuncin tafiya yajin-aikin game-gari.

Daga nan ya roƙe su da su yi zurfin tunanin abin da ƙarin albashi mai ɗimbin yawa haka zai iya haifarwa a ƙasar nan.

Gwamnatin Tarayya dai ta yi tsayuwar-gwamin-jaki, ta ce Naira 60,000 za ta iya bayarwa mafi ƙanƙantar albashi. Su kuma ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun yi fatali da wannan tayi da gwamnatin tarayya ta yi, wanda ya kira “mugun tayi.”

Yayin da NLC da TUC ta kira ƙarin da gwamnatin tarayya ta yi da “mugun tayi”, ita kuma gwamnatin tarayya ta kira farashin da ƙungiyoyin suka nemi a biya na Naira 494,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi da suna “mugun farashi.

A ranar Lahadi ɗin ce kuma Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, “buƙatar Ƙungiyar Ƙwadago ta mafi ƙarancin albashi N494,000 ya kai naira tiriliyan 9.5 duk shekara, amma ba zai ɗore ba.”

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce mafi ƙarancin albashi na ƙasa N494,000 da Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) ke nema, wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 9.5 a duk shekara, na iya gurgunta tattalin arzikin ƙasa da kuma kawo cikas ga jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200.

Idris ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga barazanar da ƙungiyar ƙwadagon ta yi na tafiya yajin aiki idan har ba a biya musu buƙatunsu ba.

Ya ce tayin na N60,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi, wanda ya kai ƙarin kashi 100 na mafi ƙarancin albashin da ake biya na shekarar 2019, ya samu karɓuwa daga ƙungiyar masu zaman kansu, wacce mamba ce na kwamitin ɓangarori uku na tattaunawar.

“Sabon tsarin albashi mafi ƙaranci na Gwamnatin Tarayya ya kai kashi 100 a kan mafi ƙarancin albashin da ake biya na shekarar 2019. Amma Ƙungiyar Ƙwadago ta buƙaci N494,000, wanda zai ƙaru da kashi 1,547 a kan albashin da ake biya.

“Mafi ƙarancin albashi N494,000 na ƙasa da ma’aikata ke nema zai kai adadin naira tiriliyan 9.5 da Gwamnatin Tarayya za ta biya.

“Ya kamata ‘yan Nijeriya su fahimci cewa, duk da cewa Gwamnatin Tarayya na son a ba ma’aikatan Nijeriya isasshen albashi, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai ƙarfafa duk wani mataki da zai kai ga asara mai ɗimbin yawa na ayyuka ba, musamman a kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ba za su iya biyan albashin da Ƙungiyar Ƙwadago ta nema ba,” inji shi.

Ministan ya ce duk da cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta damu da albashin ma’aikata kusan miliyan 1.2, Gwamnatin Tarayya ta damu da jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200 bisa la’akari da ƙa’idojinta na araha, ɗorewa, da kuma lafiyar tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.

Idris ya yi kira ga Ƙungiyar Ƙwadago da ta koma kan teburin tattaunawa tare da rungumar albashi mai ma’ana da gaskiya ga mambobinsu.

Ya ce saboda jajircewar da gwamnatin Tinubu ta yi wajen kyautata rayuwar ma’aikata, za a ci gaba da bayar da albashin ma’aikatan tarayya N35,000 har sai an ɓullo da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

People are also reading