Home Back

Abinda Ya kamata ku Sani Game Da Sabuwar Shugabar Jami’ar Abuja

leadership.ng 5 days ago
Abinda Ya kamata ku Sani Game Da Sabuwar Shugabar Jami’ar Abuja

An naɗa Farfesa Aisha Sani Mai kuɗi mai shekara 41 a Duniya a matsayin shugabar riƙo ta jami’ar Abuja. A tarihi dai ita ce mafi ƙarancin shekaru da ta riƙe wannan babban matsayi.

Ga Wasu Daga Cikin Abinda Ya Kamata Ku Sani Akanta

An haifi Farfesa Mai kuɗi a ranar 31 ga Janairu, 1983, a Zaria ta Jihar Kaduna, da ke Arewa maso yammacin Nijeriya.

Ta sami digiri na farko a fannin shari’a (LLB) a Jami’ar Reading da kuma Babban Digiri a Makarantar koyon tattalin arziki ta London da ke Burtaniya.

Bayan ta dawo Najeriya, ta halarci Makarantar koyon aikin Shari’a da ke Abuja domin samun zama Lauya. Daga nan ta samu digirin digirgir a fannin shari’a a Jami’ar Abuja.

Farfesa Mai kuɗi ta fara aiki ne a shekarar 2007 a lokacin da ta shiga aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a sashin shari’a na kamfanin Mai na ƙasa (NNPC).

Daga nan ta fara aiki da jami’ar Abuja a matsayin Malama.

People are also reading