"Lamarin Ya Yi Muni" Ƴan Bindiga Sun Kewaye Gari Guda, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Angwar Danko da ke mazabar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun tilasta wa wadanda gomman mutanen da suke ƙoƙarin yin garkuwa da su, su shiga daji.
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindiga da yawa ne suka mamaye garin da misalin karfe 6 na yammacin ranar Laraba, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganau sun bayyana cewa yanzu haka ƴan bindigan sun fara tafiya da mutanen kauyen maza da mata zuwa cikin daji.
Yahaya Musa Dan Salio, wakilin gundumar Kakangi a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa har yanzu bai samu cikakken bayani ba dangane da adadin mutanen kauyen da aka sace amma ya tabbatar da cewa suna da yawa.
“Yanzu na samu kira daga yankin, inda aka sanar da ni cewa an yi garkuwa da mutane da dama.
"Ƴan bindigar sun kewaye kauyen, kuma a yanzu da muke magana suna can, suna kokarin tafiya da mutane zuwa cikin daji. Lamarin ya yi muni,” inji shi.
Dan Salio ya nuna damuwarsa kan faruwar lamarin inda ya ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su maza ne kuma za a iya samun asarar rayuka.
Ya kuma jadddaa buƙatar tura ƙarin jami'an tsaro su tare hanyoyi domin daƙile yunƙurin ƴan bindigar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, ya ce zai tuntubi yankin domin jin cikakken bayani kafin ya yi magana.
Asali: Legit.ng