2027: Matasan Arewa Sun Gano Shirin Kawo Cikas Ga Tinubu da 'Yan Siyasa Ke Ƙullawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Matasan kungiyar Arewa Consultative Forum (AYCF) ta nuna damuwa kan makircin wasu 'yan siyasa kan Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta ce akwai wasu 'yan siyasa a Arewa da ke neman lalata damar shugaban a zaben 2027 wurin shiga lamuran gwamnatinsa.
Shugaba kungiyar, Yerima Shettima shi ya yi wanan zargi inda ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo ayyukan ci gaba a Najeriya, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya yabawa shugaban kan irin jajirtattun ministoci da sauran mukarraban da ya nada a gwamnatinsa.
Matasan sun zargi wasu daga cikin manyan 'yan siyasa a Arewa da neman dagula lamarin siyasar Tinubu a yankin, cewar Daily Post.
Daga cikin zargin da matasan suka yi har da neman hada gwamnatin Tinubu fada da al'umma domin cimma burinsu na siyasa.
Har ila yau, Shettima ya yabawa daraktan hukumar DSS, Yusuf Bichi inda ya ce ya taimaka wurin dakile matsalolin tsaron kasar.
Ya ce Bichi ya ba da gudunmawa wurin tabbatar da zakulo bayanan sirri tare da kare Najeriya daga miyagu a ciki da wajen kasar.
Ya ce shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila ya taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da tsare-tsare gwamnatin sun ba da abin da ake nema.
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakai da za su inganta rayuwar al'ummar Najeriya.
Tinubu ya ce bai damu da wahalar da 'yan kasar za su shiga na kankanin lokaci ba idan za a samu biyan buƙata.
Shugaban ya yabawa karfin guiwar 'yan kasar inda ya ce hakan ya ke kara masa kwarin guiwa kan daukar matakai masu tsauri.
Asali: Legit.ng