Home Back

Jamus za ta ci gaba da tallafawa UNRWA

dw.com 2024/5/6
Jamus za ta ci gaba da tallafawa UNRWA
Jamus za ta ci gaba da tallafawa UNRWA

Jamus ta bayyana shirinta na ci gaba da bayar da tallafi ga hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu na Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA bayan ta dakatar a baya sakamakon zargin da Isra'ila ta yi wa wasu ma'aikatan hukumar da taimakawa kungiyar Hamas wajen kai mata hari na ranar 7 ga watan Octobar bara.

Wannan zargin dai ya sanya manyan masu bai wa hukumar tallafi guda 16 ciki har da Amirka dakatar da tallafinsu gare ta na dala miliyan 450, lamarin da ya haifar wa da babban tarnaki ga ayyaukan UNRWA a Zirin Gaza da ke fama da matsalolin jin kai.

Matakin na Jamus da ke zama ta biyu cikin manyan kasashen da ke bayar da tallafin ya biyo bayan rahoton da binciken tsohuwar ministan harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna da ya wanke ma'aikatan daga wannan zargin.

A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta fitar, ta bukaci UNRWA da ta gaggauta aiwatar da shawarwarin da rahoton binciken ya fitar da ya hada da inganta ayyukanta na cikin gida.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, gwamnatin Jamus za ta ci gaba da hadi gwiwa da UNRWA a Gaza a daidai lokacin da kasashen Autraliya da Kanada da Sweden da Japan suka shirya yin hakan.

People are also reading