Home Back

Ana Tsaka da Shari’ar Masarautun Kano, Dubban Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Bidiyo

legit.ng 2024/6/28
  • Yayin da ake tsaka da shari’ar masarautu a kotu, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga Kanawa bayan sallar Juma’a
  • Aminu Ado ya gudanar da sallar Juma’a a yau a masallacinsa da ke fadar Nasarawa kamar yadda ya yi a makon jiya bayan tube shi daga karaga
  • Aminu Ado ya samu tarba daga dubban masoya wadanda suka yi dandazo domin nuna masa goyon bayan duk da umarnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake gudanar da sallar Juma’a a yau 7 ga watan Yuni a jihar.

Dubban jama’a ne suka tarbi sarkin yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma’a duk da shari’ar da ake yi.

Faifan bidiyon wanda Masarautar Kano ta wallafa a shafin X, an gano dubban masoya tare da Aminu Ado.

A makon da ya gabata ma, Aminu Ado ya gudanar da sallar Juma’a a masallacin fadarsa da ke Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yi zama kan masarautun Kano

Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da shari’a kan masarautun Kano wanda Majalisar jihar ta rusa.

A jiya Alhamsi 6 ga watan Yuni, kotu ta yi zama kan shari’ar masarautun bayan Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da korafi.

Dan Agundi ya maka Majalisar Jihar da kuma Gwamna Abba Kabir bayan rushe masaurautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Karin bayani na tafe…

Asali: Legit.ng

People are also reading