Home Back

Man United ta amince ta saki Bruno, Kevin de Bruyne na daf da komawa Saudiyya

bbc.com 2024/10/6
.

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta amince Bruno Fernandes ya shiga tataunawar komawa Saudi Arabia, Kevin de Bruyne na Manchester City ya amince da komawa Al-Ittihad, yayin da Arsenal ta amince da kwantiragin Riccardo Calafiori.

Manchester United ta bai wa dan wasan tsakiya Bruno Fernandes, mai shekara 29 izinin fara tattaunawa da Saudi Arabiya, inda kungiyoyi biyu na gasar kasar ke zawarcin dan wasan na Portugal. (TeamTalk)

Dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne, mai shekara 33, ya "amince da yarjejeniyar baka" ta koma kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya, kuma yanzu ya rage ga zakarun gasar Premier su amince da tafiyar dan kasar Belgium din. (TeamTalk)

Liverpool na fatan dan wasan gaban Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya idan kwantiraginsa ya kare a shekarar 2025. (Mirror)

Leicester City na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Fulham Bobby de Cordova-Reid, mai shekara 31, za a duba lafiyar dan kasar Jamaican daga bsani. (Telegraph)

Dan wasan tsakiya na Aston Villa Philippe Coutinho zai koma kungiyar Vasco da Gama nan ba da jimawa ba, bayan tattaunawa mai tsawo kan ko za a iya soke kwantiragin dan kasar Brazil din mai shekaru 32. (Birmingham Live)

Arsenal ta amince da sharuddan kwantiragin daukar dan wasan bayan Italiya da Bologna Riccardo Calafiori har zuwa shekarar 2029, amma har yanzu kungiyoyin na bukatar amincewa da farashin dan wasan mai shekaru 22. (Fabrizio Romano)

West Ham na son siyan dan wasan gaban Villarreal Alexander Sorloth, mai shekara 28. (AS Spanish)

An yi watsi da tayin £42m da Chelsea ta yi wa dan wasan gaban Atletico Madrid Samu Omorodion, mai shekara 20, saboda kulob din na son a kalla fan miliyan 70 kan dan kasar Spain DIN. (Sun)

Luton Town da Oxford United da kuma Bristol City duk suna sha'awar daukar dan wasan Tottenham dan asalin Ireland Jamie Donley, mai shekara 19, a matsayin aro na tsawon kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)

Arsenal na shirin siyar da dan wasan gaban Demark Mika Biereth, mai shekara 21, kan fan miliyan 4 ga Sturm Graz ta Austria. (Standard)

Manchester United da Crystal Palace da kuma Tottenham Hotspur na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiya na Hull City Jaden Philogene, mai shekara 22. (TeamTalk)

Barcelona na duba yiwuwar sake siyan dan wasan bayan Brazil Emerson Royal mai shekaru 25 daga Tottenham Hotspur. (Mundo Deportivo Spanish)

People are also reading