Home Back

Spain ta ceto 'yan ci-rani 516 daga Afirka a tsibirin Canary

dw.com 2024/7/5
Hoto: Europa Press/AP Photo/picture alliance

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Spain ta samu nasarar ceto 'yan ci-rani 516 'yan Afirka a tsibirin Canary, lokacin da suke yunkurin tsallakawa kasar ta cikin kwale-kwalen ruwa guda 5.

'Yan ci-ranin da suka hada da jarirai da kananan yara, sun shaidawa hukumomin Spain cewa 12 daga cikinsu sun mutu a kan hanya, inda suka jefa gawarwakinsu cikin ruwa, yayin da wata mata kuma ta haihu a kan hanya.

Ma'aikatar harkokin wajen Spain ta ce a watanni biyar na farkon wannan shekara ta 2024, 'yan ci-rani dubu ashirin da daya ne suka shiga kasar ta cikin ruwa, lamarin da ke nuna karin kashi 136 cikin 100 a kan na bara.

People are also reading