Home Back

Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya(2)

leadership.ng 2024/10/5
ilimi

Wani masani kuma kwararre a fannin koyo da koyarwa, sannan kuma hamshakin marubuci, Michael Omisore ya bayyana nasa dalilin na rashin samun malamai a wannan fanni na manayan darussa biyu; lissafi da kuma turanci, inda ya ce; hakan yana nuni da irin rikon sakainar kashin da ake yi wa aikin koyarwa a tsakanin al’umma.

“Darussan da dole ne sai dalibai sun samu nasara akansu, me zai sa ba za mu dauki malaman darussan, don cike wannan gurbi ba?”.

Ya ce, “Ina yin hulda da daruruwan masu nakarantu nasu na kansu a fadin tarayyar Nijeriya, wasu daga cikinsu na tambaya ta ko zan sama masu malaman Turanci gwanaye wadanda za su dauka aiki, wadansu ma har wajen zama za su ba wa malaman suka dauka.

“Don haka, me yasa ba ma daukar kwararru wadanda suke neman wannan aiki, tunda muna da wadanda suke da satifiket na kammala karatun NCE masu neman aikin yi, musamman wadabda suka karanta wadannan darussa na LIssafi da Turanci ko darussan da suke da alaka da su?”.

“Ko shakka babu, ana iya gano wadannan dalilai ta bangarori uku; yadda aka nuna lamarin ilimi a halin yanzu ba shi da wani muhimmanci, dole ne mu yi watsi da hakan, idan har ana so a dawo da martabar aikin koyarwa,” in ji shi.

Albashin Malaman Makarantu
Kamar yadda Hausawa ke cewa, ladan malamin makaranta sai a lahira zai same shi, wannan lamari ko kadan ba haka yake ba. Dalili kuwa, ko me aka bai wa malamin makaranta; ba a biya shi ba, don kuwa ya dace a tuna da cewa shi ma yana da matsalolin da suke bukatar magani.

Kamar yadda aka sani ne cewa, babban aikin malamin makaranta shi ne koyarwa, amma albashinsa bai taka kara ya karya ba, duk da cewa abin ba a kan malamin makarantar kadai ya tsaya ba; sannan akwai wadansu abubuwa masu amfani, amma mutane na nuna kamar ba su san amfanin nasa ba.

Abin da marubucin wannan makala ke kallo shi ne, idan ana maganar albashi, shi ne abin da ya kamata ma’aikaci ya yi tinkaho da shi.

Misali, da zarar an dauki ma’aikaci aiki; a matsayinsa na malamin Turanci; a kan yi alkawari za a rika ba shi albashin Naira 50,000 a kowane wata, wannan shi ne abin da zai rika sa ran gani matsayin albashi kowane wata.

Idan ya fara aikin shekara daya zuwa biyu aka kuma samun kari, za a yi tsammanin samun karin wannan albashi, idan kuma ba a samu ba sai abubuwa su fara canzawa, musamman idan mai makarantar ya ki yin karin albashin da ya kamata ya yi, malamin na iya zuwa wani wuri daban neman wani aikin koyarwar ga kuma kwarewar da ya samu ta aiki a wannan wurin.

Saboda haka, idan ya samu wata makarantar ana iya biyan sa kimanin Naira 75,000, ko kuma albashin ya zarce na wancan makarantar da ya bari. Malaman Turanci da na Lissafi, ana matukar bukatar su idan kuma har aka dace sun san darussan sosai, suna iya samun aiki a kowane lokaci tare da albashi mai tsoka lokaci zuwa lokaci.

Omisore ya kara da cewa, a nasa ganin abu na biyu bayan wannan albashi shi ne, yadda su malaman suka dauki lamarin koyarwa a matsayin aiki ne kawai; ba abin da suka karanta a makaranta domin su rayu da shi. A cewar tasa, wannan lamari na matukar damun sa idan ya ga malamai suna neman hada kansu da Injiniyoyi ko Akantoci ko kuma Lauyoyi, duk da cewa fa su ne suka zaba wa kansu wannan fanni da suka karanta, amma kuwa sun buge da hange-hange wasu daban.

Wasu malaman na yi wa wannan lamari na koyarwa kallon albashi ne kadai, ba sa kallon albarkar da ke cikin aikin na koyarwa da kuma irin kwarewar da suke samu a kan aikin, wanda ta hakan kuma wata damar daban za ta iya samuwa.

People are also reading