Home Back

Ibadar Azumin Watan Ramalan Da Taimakon Bayin Allah Domin Rage Masu Radadin Matsin Rayuwa, Daga Imam Murtadha Gusau

premiumtimesng.com 2024/4/29
Sabbin dokokin shiga masallatai da Coci-Coci 8 da hukumar NCDC ta fitar
Barnawa Juma'at Mosque Kaduna

Da Sunan Allah, Mai Rahamah, Mai Jin Kai

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh

Ya ‘yan uwana masu girma, kamar yadda kuka sani ne, Allah cikin ikon sa, ya kaddari watan azumin Ramalan ya gabato, kuma shine wata na tara a lissafin watannin Musulunci guda goma sha biyu; kuma a cikin sa ne Musulmi a duk fadin duniya suke gudanar da Ibadar azumi mai girma, tsawon kwanaki ashirin da tara (29) ko talatin (30), dogaro da yadda lissafin ganin wata ya kama.

Dukkan Musulmi ya sani, wannan wata mai daraja yana dauke da dimbin falala da daraja, da albarka da rahamar Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala. Don haka yake da muhimmanci ga dukkan al’ummar Musulmi, a ko’ina suke cikin duniya, su gudanar da ayukkan Ibadah da neman lada, don samun gafara da rahamar Allah Madaukakin Sarki.

Bugu da kari, watan Ramadan yana dauke da muhimman abubuwa na tarihi a addinin musulunci, masu tasiri a rayuwar Musulumi baki daya. Wannan a takaice kenan.

Ya ku bayin Allah! Idan ance azumi a harshen larabci shine: “Kamewa”, amma a shari’ah azumi shine: “Kamewa da niyyar Ibadah, daga barin ci da sha da saduwa da iyali da kuma sauran abubuwa masu karya azumi, daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.”

Allah madaukaki ya wajabta azumin watan Ramalan ga al’ummar Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda ya wajabta shi ga sauran al’ummomin da suka gabata. Allah madaukakin Sarki yana cewa:

“Ya ku wadanda suka yi imani! an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku,tsammanin zaku samu takawa (wato tsoron Allah).” [Suratul Bakarah: 183]

Kuma an farlanta azumi ne a watan Sha’aban, shekara ta biyu bayan hijrah.

Ya ku al’ummar musulmi! Ku sani, azumi yana da fa’idoji da dama. Misali, akwai fa’idoji na zuciya, akwai na zamantakewa, akwai na lafiya. Sune kamar haka:

1. Yana daga fa’idar azumi ta zuciya (wato ruhi), yana taimakawa wurin samun hakuri da juriya, da kuma karfafuwa a kan hakan. Yana samar da kamun kai da kuma taimakawa kai; haka kuma yana samar da kare zuciya daga sabawa Allah mai girma da daukaka, da kuma dora ta akan tarbiyyar hakan.

2. Daga cikin fai’dar azumi ta zamantakewa kuwa, azumi yana koyar da musulmi tsari, da kokari, da son adalci da tsayuwa akan gaskiya; kuma yana sa wa mumini tausayi da dabi’u masu kyau, kamar yadda mutane ke kamewa daga sharri da kuma dukkan abin da yake barazana ne a gare su.

3. Yana daga cikin fa’idar azumi, yana taimakawa wurin samun lafiyar jiki: azumi yana tsarkake kayan ciki, kuma yana gyara hanji, yana kyautata jiki daga kamuwa da cututtuka, kuma yana tsane jiki daga yawan mai (wato kitse), da nauyin jiki.

Sannan watan Ramalan yana tabbata ne da dayan abubuwa guda biyu:

Na farko: Cikar watan da ya gabace shi kwana talatin, wato watan Sha’aban. Idan Sha’aban ya cika kwana talatin, rana ta talatin da daya yini ne na Ramalan kai tsaye.

Na Biyu: Ganin jinjirin watan Ramalan. Idan aka ga jinjirin watan Ramalan a daren talatin na wannan wata na Sha’aban, wato ashirin da tara ga wata. Domin fadin Allah madaukakin Sarki:

“Duk wanda ya shaidi (shigar) watan Ramalan to ya azumce shi.” [Suratul Bakarah: 185]

Haka kuma da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a inda yace:

“Idan ku ka ga jinjirin wata to ku dauki azumi, kuma idan ku ka gan shi ku ajiye azumi, idan kuma an boye maku shi ta (dalilin giragizai) to ku cika shi talatin.” [Bukhari da Muslim]

Kuma idan mutanen gari suka ga watan azumi ya wajaba gare su. Kamar yadda fitar wata yana sabawa. Misali, fitar wata a yankin Asiya daban yake da yadda fitar shi yake a yankin Turai da Afrika, kuma ba haka yake ba a latin Amirka misali. Da haka ne ko wane yanki da bangare na duniya suke da hukuncin da ya kebance su game da ganin wata. Amma idan kuma al’ummar musulmai baki daya suka yi azumi da ganin wata daya to wannan shine abin da yafi kyautatuwa, tare da bayyana hadin kai da kuma ‘yan uwantakar musulunci.

Kuma ganin watan mutum daya adali ya wadatar, ko mutum biyu, kamar a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya karbi ganin watan mutum daya na Ramalan (Muslim ne ya ruwaito shi). Amma na ajiye azumi (wato watan Sallah) ba ya tabbata sai da ganin adilai biyu, kamar yadda Manzon Allah (SAW) bai karbi ganin watan adili daya ba a lokacin ajiye azumi.

An wajabta muna azumi kamar yadda yazo a cikin Alkur’ani da Hadisai da kuma Ijma’in malamai. Kuma azumi daya ne daga cikin rukunnan musulunci guda biyar. Allah Ta’ala yace:

“Watan Ramalan shine watan da aka saukar da Alkur’ani a cikin sa, yana mai shiryarwa ga mutane da kuma bayyanar da shiriya da kuma bambancewa (tsakanin karya da gaskiya), duk wanda ya shaida ganin watan daga cikin ku sai ya azumce shi…”. [Suratul Bakarah: 185]

Kuma Manzon Allah (SAW) yace:

“An gina musulunci akan abubuwa guda biyar: Shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsaida Sallah, da bayar da Zakkah, da ziyartar dakin Allah (wato aikin Hajji), da kuma azumin watan Ramalan.” [Bukhari da Muslim]

Azumin watan Ramalan yana da rukunnai kamar haka:

1. Niyyah: Ita ce kudurtawa a cikin zuciya, akan kamewa domin bin umarnin Allah, da neman kusanci zuwa gare shi, domin fadin sa:

“Dukkan aiki na Ibadah sai da niyyah …..” [Bukhari da Muslim]

2. Kamewa: Shine nisantar duk wani abin da zai
karya azumi na ci ko sha ko saduwa da sauran su.

3. Lokaci: Abin nufi shine yini, shine kuma daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Sharudan wajabcin azumi guda hudu ne kamar haka:

1. Musulunci; 2. Balaga; 3. Hankali da 4. Samun Iko.

Sannan kuma sharadi ne mace ta samu tsarkaka daga jinin al’ada da jinin haihuwa.

Sharuddan Ingancin Azumi, sune kamar haka:

1. Musulunci; 2. Daukar niyyah da dare; 3. Wayo; 4. Yankewar jinin al’ada da 5. Yankewar jinin haihuwa (wato jinin biki).

Azumi yana da sunnoni kamar haka:

1. Gaggauta bude baki. Shine bude-baki da zarar an tabbatar da faduwar rana.

2. Ana so abin bude baki ya kasance danyen dabino ko busasshen dabino ko kuma ruwa. Wanda yafi a cikin ukun nan shine na farko da na karshe kuma shine na karshen su, mai bi masu kuma shine na biyun, an so a bude baki da wutiri, (wato mara).

3. Addu’a yayin bude baki. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yin addu’a a lokacin bude-bakinsa.

4. Cin sahur, har zuwa karshen dare, da niyyar azumi.

5. Jinkirta sahur, har zuwa tsagin dare na karshe.

Kuma an karhantawa mai azumi wasu al’amurra wadanda ke iya jawo bacin azumi, amma da yake su a karankansu ba sa karya azumi kai-tsaye, sune kamar haka:

1. Kai makura wurin kurkurar baki da shaka ruwa a hanci lokacin alwala.

2. Sumbata, ita tana tasiri ta janyo sha’awa wadda ke bata azumi, ta dalilin fitowar maziyi ko ta saduwa ta yadda za ta wajabta kaffarah.

3. Yawan kallon mata don jin sha’awa.

4. Tunani a wurin sha’anin saduwa.

5. Shafa mace da hannu ko rungumarta.

Sannan ya halatta mutum ya ajiye azumi saboda uzuri kamar haka:

1. Ya wajaba ga mai al’ada da mai jinin haihuwa su ajiye azumi.

2. Wanda yake so ya tsamo wani daga halaka, da sauransu.

3. Matafiyi an halasta masa yin sallar kasru, kuma an sunnanta masa ajiye azumi.

4. Marar lafiya wanda yake tsoron cutuwa.

5. Mazaunin gida wanda yayi tafiya da rana, amma abunda yafi shine yayi azumi don fita daga cikin sabani.

6. Mace mai ciki da mai shayarwa, wadanda suka ji tsoron cutarwa a karankansu, ko a kan dan da ke cikin su, koda sun ajiye azumi don tsoron ‘ya’yan su, waliyan su za su ciyar da miskini a ko wane yini, bayan haka za su rama azumi (amma a wurin wasu malaman babu rama azumin, ciyarwa kawai za su yi).

Abubuwan da suke bata azumi sune kamar haka:

1. Yin riddah (wato fita daga addinin musulunci); 2. Mutuwa; 3. Niyyar karya azumi; 4. Kokwanto game da azumi; 5. Kirkiro amai da gangan; 6. Yin allura mai sa koshi; 7. Fitowar jinin al’ada ko na haihuwa; 8. Hadiye kaki idan ya kawo baki; 9. Yin kaho: mai yi da wanda aka yi wa (amma a wani zancen, yin kaho baya karya azumi); 10. Fitar maniyyi ta dalilin kallo mai yawa; 11. Fitar maniyi ko maziyi ta hanyar sumbanta ko shafa ko istimna’i ko runguma ba tare da saduwa ba; 12. Da duk abun da ya isa zuwa makoshi ko makogwaro ko kwakwalwa na wani abu mai ruwa ko waninsa.

Sannan duk wanda ya sadu da matarshi a cikin watan Ramalan ta gaba ko ta baya, to ramako da kaffarah sun wajaba a kanshi, idan da gangan ya aikata. In kuma ya manta ne, to azumin shi bai baci ba, kuma babu ramako balle kaffarah a kansa. Idan aka tilasta wa mace saduwa da rana cikin watan Ramalan, ko ta jahilci hukuncin yin hakan, ko ta manta, to azumin ta yana nan. Idan kuma an tilasta mata ne to ramako ya wajaba a kan ta kawai, idan kuma da gangan ta aikata to kaffarah da ramako sun wajaba a kanta.

Kaffarah ita ce ‘yanta baiwa. Idan kuma babu sai ayi azumi na tsawon wata biyu a jere, idan kuma ba ya yiwuwa sai a ciyar da miskinai sittin, idan kuma ba ya da iko to an dauke masa.

Idan mutum ya sadu da matarsa ta dubura, ramako ya wajaba a kansa da kuma tuba zuwa ga Allah.

Sunnah ne ramakon azumin Ramalan cikin gaggawa, kuma ayi shi a jere, idan kuma ya jinkirta har wani Ramalan ba tare da wani uzuri ba, to ramako da ciyarwa sun wajaba a gare shi a kowane yini.

Sannan duk wanda ya mutu, kuma yana da bashin azumin alwashi ko alwashin Hajji, to waliyan sa su rama mishi.

An so yin azumin nafilah na wadannan ranaku kamar haka:

1. Azumin ranar Arafah ga wanda ba mahajjaci ba. Ita ce ranar tara ga watan Zul-Hajji.

2. Azumin tara da goma, ko goma da sha-daya na watan Muharram.

3. Azumin kwanaki shida na watan shawwal (wato Sittu Shawwal).

4. Goman farko na watan Zul-Hajji.

5. Watan Muharram.

6. Ranakun tsakiya na kowanne wata sune: sha-uku da sha-hudu da sha-biyar.

7. Ranakun litinin da alhamis.

8. Azumin kwana daya da hutun kwana daya.

9. Azumi ga wanda ba ya da karfin yin aure.

2. Azumin da aka hana yi, sune kamar haka:

1. Azumin ranar Arafah ga mai aikin Hajji.

2. Kebe azumin ranar juma’ah kawai (wato ba tare da hada alhamis ko asabar ba).

3. Yin azumi Karshen Sha’aban.

Kuma ya kamata mu sani, yin azumi a wadannan ranaku an hana ne hani na karhanci.

Amma wadanda aka hana hani na haramci, sune kamar haka:

1. Azumin Dore: shine hada azumin kwana biyu ba tare da shan ruwa ba.

2. Yin azumi ranar kokwanto (wato ranar shakka).

3. Yin azumin shekara ba tare da hutawa ba.

4. Yin azumin mace na nafilah ba tare da izinin mijinta ba, alhali yana gida.

Azumin da aka haramta yi baki daya, sune kamar haka:

1. Yin azumi ranar bukukuwan Sallah karama ko Sallah babba.

2. Yin azumin ranakun shanya nama (ayyamut-tashrik). Sune ranakun 11, da 12, da 13 na watan Zul-Hajji, ga wanda ba mai tamattu’i da bai sami fidiya ba.

3. Ranakun al’ada da jinin haihuwa ga mata.

4. Azumin mara lafiya, rashin lafiya mai tsanani wadda yake ji wa kansa tsoron halaka.

Kuma ya kamata ga duk musulmin kwarai yayi shiri na musamman domin samun amfani da fa’ida da falalar watan Ramalan. Idan ba mu yiwa kan mu tsarin da ya kamata ba, to Ramalan zai zo ya wuce ba tare da mun aikata alherin komai ba. Mala’ika Jibril yayi addu’a cewa:

“Ya Allah duk wanda Ramalan yazo ya wuce bai yi aikin da Allah zai gafarta masa ba ka turbuda hancinsa a wuta, kuma Annabi (SAW) yace amin.”

Ya ku bayin Allah! Daga cikin manyan Ibadu da ake so dukkan Musulmi ya aiwatar a cikin watan Ramalan don neman kusanci ga Allah, kuma Ibadun da suke da lada mai yawa, sun haɗa da ciyar da bayin Allah mabukata a cikin watan azumi. Wato baiwa mai azumi abinci, ko a tanadar masa abin da zai yi buɗa-baki da shi, na ci ko na sha, da abin da zai yi sahur da shi gwargwadon abin da mutum zai iya yi, tare da kyakkaywar niyar neman kusanci ga Allah Madaukakin Sarki.

Misali, wani zai iya raba kayan abinci wadanda ba’a dafa ba. Kamar shinkafa, gero, dawa, masara, wake, suga da sauran su. wani zai iya yin kunu da ƙosai, wani kuma zai iya yin koko, wani zai iya yin lamurje, zoɓorodo ko kunun zaki, ko kunun aya. Wani kuma zai iya dafa shinkafa, wani kuma zai iya bayar da ruwan sanyi, wani kuma zai iya bayar da wani abu na ci ko na sha. Kowa dai gwargwadon abin da zai iya bayarwa, da adadin mutanen da ya ga zai iya ciyarwa. Misali, wani kullum zai iya yin abincin mutum goma, wani na mutum ashirin, wani ma fiye da haka. Ma’ana, da abincin da ruwan shan na mutum goma, ko ashirin ko talatin, ko fiye da haka. Ka ga idan kullum zai iya ciyar da mutum goma, idan Ramalan ya wuce tamkar ya ciyar da mutum ɗari uku kenan. Wani kuma zai iya ciyar da mutum biyar, kullum har ƙarshen Ramalan. Wanda ya ciyar da mutum biyar kullum har ƙarshen Ramalan, kamar ya ciyar da mutum ɗari da hamsin kenan.

Idan kuma abincin mutum ɗaya tak zai iya ciyarwa a kullum, ka ga ya ciyar da mutum talatin kenan.

Falalar da ke cikin aikata hakan ita ce, wanda duk ya ciyar ko ya taimakawa mai azumi yayi buɗa baki ko yayi sahur, Allah Subhanahu wa ta’ala zai ba shi ladan yayi azumi cikakke, wato kenan idan ka ciyar da mutum biyu za’a ba ka ladar azumi biyu, idan ka ciyar da mutum uku za’a ba ka ladar azumi uku. Wato kenan adadin mutanen da ka ciyar a watan Ramalan shine adadin ladar azumin da za’a ba ka, ban da ladan naka. Azumin da ka yi shi ma yana nan, sai a haɗa maka tare da waɗancan.

Don haka ana buƙatar duk wani Musulmi ya zage damtse yayi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ciyarwa, domin wata ne na falala da samun lada, musamman ma idan muka kalli falalar da ciyarwa take da shi.

A cikin siffofin da Allah Madaukaki ya lissafa na mutanen kirki, wadanda za su shiga Aljannah, akwai waɗanda Allah ya bayyana su inda yake cewa:

“Suna ciyar da abinci irin wanda suke so, suna ciyar da shi ga miskini da maraya da kuma ribatacce. (Suna cewa), Lallai haƙiƙa mu muna ciyar da ku ne domin neman yardar Allah, ba ma neman sakamako a gare ku, kuma ba ma neman ku gode mana. Mun yi haka ne saboda muna jin tsoron wata rana da Ubangiji zai kawo ta mai ɗaure fuska. Sai Allah ya tsare su sharrin wannan rana.” (saboda imaninsu da ciyarwa da suke yi).

Sannan ciyar da abinci da shayar da ruwa da kuma taimakon mai jin yunwa suna daga cikin abin da zasu jawo mutum yazo daga cikin ‘yan dama-dama da ‘yan gaba-gaba a ranar Alƙiyama.

Sannan daga cikin dalilan da suke jawo mutum ya shiga Aljannah, akwai ciyar da abinci, musamman ga mai azumi ko wani mai jin yunwa.

Haka nan ya tabbata daga abin da yake tserar da mutum daga shiga wuta akwai ciyar da dabino, wato ko da tsagin dabino ne.

Sannan babu aikin da Allah Yake so fiye da irin waɗannan ayyukan guda huɗu. Wato ka sanya mutum cikin farin ciki, ka yaye masa damuwa, ka kore masa yunwa, ka biya masa bashi.

Haka nan dai ciyar da abinci yana daga cikin ayyuka na gaba-gaba, wadanda Allah Yake so.

Kuma ciyarwa tana daga cikin abin da yake ƙara kusanta mutum ga Allah.

Haka nan ana ninninka lada ninkin-baninki ga wanda yake ciyarwa domin Allah.

Haka nan da wannan ciyarwar ake samun taimakon Allah.

Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:

“Sifar waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwaya ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kowace zangarniya akwai ƙwaya ɗari. Kuma Allah Yana riɓanyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani.” [Suratul Baƙara: 261]

Ya ku bayin Allah! Lallai matukar muna son rahamar Allah da tausayin sa a gare mu, da kuma samun nasara a cikin duk wani abu da muka sa a gaba, to ya zama wajibi gwamnatocin mu da ‘yan siyasa, da ‘yan kasuwa da masu hali, su ciyar da talakawa da gajiyayyu, da marayu da matalauta, da marasa hali, albarkacin wannan wata na Ramalan, domin samun sauƙin radadin matsin rayuwa, da samun saukin wannan hali da ake ciki na kunci.

Ku sani, duk wanda kuka taimakawa, matuƙar kunyi domin Allah, da Ikhlasi, to tabbas kuma Allah Maɗaukakin Sarki zai taimaka maku ta hanyar da ba kuyi tsammani ba.

Kuyi koƙari ku ciyar cikin azumin nan. Kuyi kokari ku cusa farin ciki a cikin zuƙatan bayin Allah. Idan kun yi haka, kuma sai ku wayi gari Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya sanya maku farin ciki marar misaltuwa a cikin zukatan ku.

Allah ya baku ikon taimakon bayin Allah, amin.

Ya ku bayin Allah! Duk da wannan bayani na falalar ciyarwa, da ya gabata, a yau fa akwai Musulmi da dama da suka dauka cewa Allah ba ya bukatar komai daga gare su, don haka zaka ga suna ta Ibadah ta yau da kullum, da ta mako, ko wata, ba tare da sun tsaya sun yi dogon tunani ba, kuma ba tare da sun sadaukar da komai na dukiyarsu domin amfanin jama’arsu da sauran wadanda suke cikin kunci ba.

Irin wadannan Musulmi suna ganin cewa sallarsu da azuminsu da hajjinsu da umararsu kadai sun isa su samar masu da yardar Allah, tare da samun gidan Aljannah.

Wasu daga cikinsu kuwa, imaninsu a baka kawai yake.

Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa ta’ala yasa su gane, kuma ya basu ikon taimakon bayin Allah, amin.

Ya Allah ka sadar da mu da Ramalan kuma ka bamu iko da damar aikata alheri a cikin sa, kuma ka karba daga gare mu, ka sanya mu cikin bayin da za ka ‘yan ta daga wuta.

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawarka a koda yaushe. Ka kawo muna zaman lafiya, da ci gaba mai amfani a kasar mu Najeriya.

Ya Allah ka bamu lafiya da zama lafiya a cikin kasashen mu da garuruwan mu.

Ya Allah ka kare mu da zuri’ar mu daga cututtuka da fitintinun zamani.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunubanmu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala da yaci gaba da kyautata muna, ya kawo muna mafita ta alkhairi a cikin dukkanin al’amurran mu, amin.

 
People are also reading