Home Back

EFCC Ta Bankado Makarkashiyar da Ake Kulla Mata, Ta Yi Gargadi

legit.ng 3 days ago
  • Hukumar EFCC wacce ke yaƙi da masu aikata rashin gaskiya a Najeriya ta ce akwai masu shirin yin zanga-zanga kan ayyukanta
  • EFCC ta bayyana cewa wasu gurɓatattu ne da hukumar ke bincika ko tuhuma ke son yin amfani da zanga-zangar domin kawo rikici a ƙasa
  • Ta bayyana cewa ko kaɗan ba za ta bari a yiwa doka karan tsaye ba musamman a ofisoshinta da ke faɗin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta sanar da jama'a wata maƙarƙashiya da ake ƙulla mata.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa akwai wani shiri da wasu ƙungiyoyi ke yi domin tayar da zanga-zangar nuna adawa da hukumar.

EFCC ta bankado shirin zanga-zanga kan ayyukanta
EFCC ta ce ana shirin shirya zanga-zanga kan ayyukanta Hoto: @OfficialEFCC Asali: Facebook

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Dele Oyewale, ya sanya a shafin X na hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane shiri ake yi kan EFCC?

EFCC ta ce a cikin ƴan kwanakin da suka gabata, ƙungiyoyin sun yi kamfen sosai a shafukan sada zumunta, inda suka ɗauki haziƙan matasa ƴan Najeriya, ciki har da ɗalibai domin nuna adawa da ayyukanta.

Ta ce ana ci gaba da gudanar da wannan kamfen ɗin ne domin nuna turjiya kan ayyukan hukumar musamman ta fuskar aiwatar da dokokin da suka shafi aikata laifukan yanar gizo.

"Hukumar, duk da cewa ba ta nuna adawa da zanga-zangar da ƴan ƙasa ke da ikon yi ba, ta damu bisa shaidun da ke nuna wani shiri na wasu gurɓatattu da hukumar ke bincika ko tuhuma domin yin amfani da zanga-zangar su tayar da hargitsi a ƙasa."
"A matsayin hukumar tabbatar da doka da oda, hukumar ba za ta amince da duk wani shirin yiwa doka karan tsaye ba a ko’ina a cikin ƙasar nan musamman a kusa da ofisoshinta a faɗin Najeriya."
"EFCC, tare da sauran hukumomin ​​tsaro na aiki domin ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron Najeriya."

- Dele Oyewale

Shugaban EFCC ya koka kan sata a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, Ola Olukoyede, ya koka kan girman satar da wasu masu cin hanci da rashawa ke yi a ƙasar nan.

Ya ce ya kan kasance a cikin mamaki kan yadda har yanzu ƙasar nan ba ta durƙushe ba duk lokacin da ya duba takardun shari'a ya ga irin kuɗaɗen da aka sata.

Asali: Legit.ng

People are also reading