Home Back

Najeriya: Tsadar rayuwar ta janyo karuwar fashi da makami

dw.com 2024/7/4
Hoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

 Mata da dama da mazajensu suka bar musu nauyin ciyar da gida ,da sauran dawainiya da wasu daga cikin ‘ya'yan su da suka fada a cikin wannan yanayi, sun bayyana takaicin su bisa ga yadda ‘ya'yan da suka haifa,sun zama wadanda ke cutar da al'umma da kuma jefa kasa da al'umman cikin wani yanayi. Wata uwa da ba ta so a fadi sunan ta ba, ,ta bayyayana cewa akwai kunya ganin yadda ‘ya'yan su ,suka zamo masu kisa da raunata al'umman kasa saboda abin hannnun su, ta wadannan ‘ya'yan sun dade suna   aikata abubuwan da za ta iya dangartashi da dabbanci, a saboda haka ne ta ke yin kira ga hukumomi wajan ribanya kokarin da suke yin a ceto al'umma daga ayyukan da ‘ya'yansu ke aikawa. To baya ga barayin wayar hannu ,akwai karuwar masu haurawa ta katanga suna  shiga gidajen matan aure wajan sata da tsakar dare,al'amarin da ya sanya  Ladi Auta daga unguwar Romi Kaduna,cewa abin takaici ne halin da wasu daga cikin ya'yan su suka shiga sakamakon wanan matsin rayuwa. ''A duk lokacin da mutun ya wuce ,suna zaune suna kallon sa, babu wani abin da suke yi face dai kwace da illata bil Adama da shaye-shayen muggan kwayoyin da ke illata rayuwar su.Tuni dai wata hadakar kungiyoyin tsaro na sa kai ta jIhar Kaduna Coaliation of civilian JTF suka tashi tsaye ta hanyar barbaza jami'an tsaron domin magance ayyukan wannan matasa a cewar kakakin hadakar  Comrade Sunusi Surajo.

People are also reading