Home Back

TSADAR ABINCI: Majalisar Dattawa za ta yi wa farashin abinci taron-dangi

premiumtimesng.com 2024/8/24
RIKICI KAN WURIN ZAMA A MAJALISAR DATTAWA: ‘Mu tsoffin ‘yan-alewa ne, ba sabbin-yanka-rake ba’ – Sanata Goje, Ya’u

Majalisar Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta shawo kan masifar tsadar kayan abincin da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.

An zartas da hakan bayan amincewa da ƙorafin da Sanata Sunday Karimi na Jihar Kogi ta Yamma ya yi a zauren Majalisar Dattawa, ranar Talata.

Karimi ya shaida wa Majalisa cewa farashin kayan abinci irin su shinkafa, wake, tumatir, albasa da sauran wasu da dama ya zarce buƙatun talakawan da ke noma abincin.

Ya bayyana dalilai irin su matsalar tsaro, cire tallafin fetur da karyewar darajar Naira a kasuwar canji.

Haka kuma sanatan ya bayyana yadda su kan su masu sayar da kayan abinci ke tsawwala tsada, tare da yin kira ga Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), ta haɗa kai dai Ma’aikatar Harkokin Noma domin su wayar wa masu sayar da kayan abinci kai, tare da yi masu gargaɗin abin da ka iya haifarwa a wannan yanayi na masifar tsadar kayan abinci da aka afka.

Ya kuma yi kukan cewa manoma da ke kan iyaka da wasu ƙasashe masu maƙautaka da Najeriya, sun daina sayar da kayan nan cikin Najeriya, sai su na tsallakawa maƙautan ƙasashe suna sayarwa .

Cikin sanatocin da suka ƙara wa muryar Sanata Karimi amo, har da Sanata Ali Ndume da Ahmed Wadada. Sun yi kiran gaggawa ga Gwamnatin Tarayya ta yi hanzarin taka wa wannan masifa burki, domin burkin a cewar su, ya kusan tsinkewa.

‘Za A Bai Wa Gwamnoni Takin Zamani Domin Su Raba Wa Manoma’ – Akpabio:

Shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce za a raba wa kowane gwamna lodin tirela 60 na takin zamani, sanata tirela 2, ɗan majalisar tarayya tirela 1, domin su raba wa manoma.

A ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na farfaɗo da sauƙin tsadar rayuwa, kwanan nan za a raba wa kowane gwamnan jiha lodin tirela 60 na takin zamani, domin raba wa manoma.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a majalisa a ranar Talata.

Ya ce su ma sanatoci za a bai wa kowa tirela 2 na lodin takin zamani, domin rabawa a mazaɓar sa. Haka su ma mambobin tarayya za a ba kowa lodin tirela ɗaya domin ya kasafta wa manoman mazaɓar sa.

Akpabio ya bayyana haka lokacin da yake maida jawabi kan wani koke da Sanata Sunday Karimi na Jihar Kogi ya yi, wanda ya yi kiran gaggawa ga gwamnatin tarayya ta shawo kan masifar tsadar kayan abinci.

“Za a bai wa kowace jihar lodin tirela 60 na takin zamani, haka su ma sanatoci da mambonin tarayya za a raba masu, domin su ma su raba wa mazaɓun su,” cewar Akpabio.

Sai dai kuma Akpabio ya shaida wa ‘yan jarida cewa kada su ce wannan magana daga bakin sa ta fito. Ya ce a ce shi ma ji ya yi daga bakin Shugaban Kwamitin Harkokin Noma na Majalisar Dattawa, Sanata Saliu Mustapha.

“A to, don kada gobe na yi baƙin jini a wurin gwamnoni, su ce na ari bakin su na ci masu albasa.”

People are also reading