Home Back

‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Malaman Jami’a A Jihar Katsina

leadership.ng 2024/7/3
‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Malaman Jami’a A Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza.

An rawaito cewa, an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon.

Rahotanni sun bayyana lamarin ya faru ne a GRA Dustin-Ma da misalin karfe 1:am na ranar Litinin.

An kuma rawaito cewa, ‘yan ta’addar sun afka GRAn ne da muggan makamai inda suka rika harbe-harbe a sama.

Da aka tuntubi Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai, ya ce, rundunar tana aiki tare da hadin guiwar sauran jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace.

People are also reading