Home Back

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Farmaki Masunta a Borno, an Rasa Rayukan Mutum 15

legit.ng 2024/6/18
  • Ƴan ta'adda ɗauke da makamai na ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP sun kao hari kan masunta a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno
  • Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka masunta mutum 15 lokacin da suke shirin fara kun kifi da daddare a ranar Lahadi
  • Ƴan ta'addan sun zagaye masuntan ne sannan suka jera su ɗaya bayan ɗaya kafin daga bisani suka buɗe musu wuta hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan ISWAP sun kashe masunta aƙalla 15 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:40 na dare, a lokacin da masunta ke shirin kamun kifi da daddare a yankin Tumbun Rogo Kangarwa da ke ƙaramar hukumar.

'Yan ta'addan ISWAP sun hallaka masunta a Borno
'Yan ta'addan ISWAP sun kashe masunta a Borno Hoto: @govborno Asali: Facebook

A cewar wata majiya, mayaƙan na ISWAP sun kai farmaki yankin inda suka zagaye masuntan sannan suka jera su kafin su buɗe musu wuta, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun zo ne sannan suka buɗewa mutanen mu wuta, an kashe mutum 15, yayin da sauran da suka suka yi nasarar tserewa, sun samu raunuka daban-daban kuma a halin yanzu suna samun kulawa a Cross Kauwa."

- Wani majiya

Ƴan ta'addan ISWAP na yawan kashe masunta

Tashar Channels tv ta ce daga watan Fabrairun 2024 zuwa watan Mayun 2024, ƴan ta'addan sun hallaka masunta 30 a yankin.

Wani majiya ya bayyana cewa ƴan ta'addan ISWAP su kan kai hari ga masunta idan sojoji suka tare kayan aikin su sannan su yi musu sata.

"Mun yi jana’izar mutum 15 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a safiyar ranar Litinin."
"Sun kwashe duk kifinmu. Hatta mutanen mu da yawa har yanzu ba a gansu ba, mun binciki dazuzzuka da ke kusa amma ba mu gansu ba."

- Wani majiya

Ƴan ta'adda sun datse hannun masunta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ISWAP sun yanke hannun wasu masunta biyu a garin Marte da ke jihar Borno, bayan sun zarge su da satar kifi.

Masuntan sun kasance mambobin wata babbar ƙungiya da ke gudanar da ayyukan kamun kifi a ƙarƙashin ikon ISWAP, inda suke biyansu haraji da ihisani.

Asali: Legit.ng

People are also reading