Home Back

BIDIYO: Ina goyon bayan a yi aiki da rahoton Oronsaye – Aliero

premiumtimesng.com 2024/4/28
BIDIYO: Ina goyon bayan a yi aiki da rahoton Oronsaye – Aliero

Sanatan dake wakiltar Kebbi ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aliero ya bayyana cewa ya na tare da ɓangaren shugaban Kasa Bola Tinubu game da yin aiki da rahoton Oronsaye.

Da yake tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Aliero ya ce rahoton na sa amfani matuka kuma yana goyon bayan lallai ayi aiki da wannan rahoto.

Da aka tambaye shi me ya kawo shi fadar shugaban kasa yana dan jam’iyyar Adawa, PDP kuma gwamnati mai ci APC ce, sanatan ya ce ” Tinubu aboki na ne ba tun yanzu ba. Tare muka yi gwamna, ni ina Kebbi, shi yana Legas. Mukan ba juna shawarwari a matsayin abokan juna.

 
People are also reading