Home Back

Cristiano Ronaldo Ya Tafi Saudiyya, Ya Kafa Tarihin Cin Kwallaye a Duniya

legit.ng 2024/7/1
  • Shahararren dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar kwallon kafa
  • Cristiano Ronaldo ya zama ɗan kwallo tilo da ya fi cin ƙwallo a kasashe daban-daban har guda hudu a fadin duniya
  • A yanzu haka Cristiano Ronaldo ya kafa wani tarihin a kasar Saudi Arabia inda yake buga wasa a kungiyar Al-Nassr

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama ɗan kwallo da ya shahara a kasashe hudu da ya taka leda.

CR7 ALnasr
Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallo a duniya. Hoto: Cristiano Ronaldo Asali: Facebook

Cristiano Ronaldo ya yi fice a kasashe

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa Ronaldo ya shahara da cin kwallaye a kasashen England, Spain, Italy da Saudi Arabia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu haka dan kwallon yana taka leda ne a kungiyar Al-Nassr da ke kasar Saudi Arabia bayan barin Machester a Ingila.

Tarihin da Ronaldo ya kafa a kwallo

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama ɗan kwallo na farko a duniya da ya zura kwallaye mafi yawa a ƙasashe hudu mabanbanta.

Ya kafa tarihin a kasar England a kungiyar Manchester United, a Spain a kungiyar Real Madrid, a Italy a kungiyar Juventus sai kuma a kasar Saudi Arabia a kungiyar Al-Nassr.

Ronaldo ya kafa tarihi a Al-Nassr

Har ila yau dan kwallon ya kafa tarihi a kasar Saudi Arabia a kungiyar Al-Nassr da ya ke takawa leda, rahoton Punch.

Ronaldo ya zama ɗan kwallo na farko da ya zura kwallo 35 a gasar kwallon Saudi Arabia a kakar wasa daya.

A yanzu haka dai Ronaldo ya zura kwallo 765 a shekaru 22 da ya shafe yana taka leda a kungiyoyi daban-daban.

Kuma shi ne ke rike da kambun tarihin dan kwallo da yafi zura kwallo ga kasarsa inda ya ci kwallo 128 ga kasar Portugal a wasanni 206 da ya buga.

Kudin da Ronaldo ya samu a shekara

A wani rahoton, kun ji cewa a cikin watanni 12, an ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya samu albashin dala miliyan 260.

Wannan kuwa na zuwa ne yayin da kwantiragin Ronaldo da kungiyar Al Nassr ta samawa dan wasan dala miliyan 200 a kaka daya.

Asali: Legit.ng

People are also reading