Yayin da Ake Batun Sauya Tsarin Mulki, Shettima Ya Fadi Babban Matsalar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana babban abin da Najeriya ke bukata a yanzu.
Kashim ya ce matsalar kasar ba sauya tsarin gwamnati ba ne illa samar da shugabanci nagari.
Shettima ya bayyana haka ne a yau Asabar 1 ga watan Yuni a birnin Ilorin na jihar Kwara yayin wani babban taro, cewar Daily Trust.
Wannan martani na Kashim na zuwa ne yayin da ake yada jita-jitar sauya tsarin yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya.
"Dimukradiyya na samun ci gaba ne kadai idan aka samar da shugabanci nagari da kuma bin doka da oda."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bin tsarin fira minista ba shi ya ke nuna ci gaban dimukradiyya ba kamar yadda wasu ke tunani."
"Kasashe da dama sun ruguje ne saboda rashin bin doka da kuma kin bin gaskiya tare da cin amana."
- Kashim Shettima
Shettima ya kuma karyata cewa Shugaba Tinubu ya na katsalandan a harkokin zaben da ake gudanarwa a kasar.
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murnan cika shekara daya a kan mulki.
Buhari ya roki ƴan Najeriya da su ci gaba da ba Tinubu goyon baya da hadin kai domin inganta rayuwar yan kasar.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya cika shekara daya kan mulki da ƴan kasar ke kokawa kan halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng