Home Back

Dalilin da ya sa na sauya sheƙa zuwa APC bayan shekaru 25 a PDP - Shagari

bbc.com 2024/10/5

Dalilin da ya sa na sauya sheƙa zuwa APC bayan shekaru 25 a PDP - Shagari

Minti 1 da ta wuce

Tsohon ministan ruwa a zamanin gwamnatin Olusegun Obasanjo, Barista Mukhtari Shehu Shagari kuma mataimakin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Alu Magatakardar Wamakko, ya ce dole ce ta sa ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP a jihar zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

"Dole idan ana magana akan jam'iyyar PDP, sai an ambace ni. Ni ne mutumin da gwamnana ya sauya shea amma ina matsyain mataimaki amma na ƙi bin sa. To amma yanzu na ga waɗanda ke jam'iyyar suna ganin Mukhtar ya tsare musu wani abu. Ba sa son zamana a cikin jam'iyyar.

To shi ne jama'armu suka lokaci ya yi na mu bar jam'iyyar mu je wurin da ake ganin mu da ƙima. To shi yasa muka yi wannan sauyin sheƙa." In ji Shagari.

Dangane da burinsa na siyasa ko zai yi takara ko ba zai yi ba, Mukhtari Shagari ya ce "ni yanzu ina da gwamnan da ayyukan da yake yi sun gamsar da ni. Idan ya nemi sake tsayawa takara zan mara masa baya."

Tsohon ministan ya kuma yi tsokaci dangane da shekaru 25 da Najeriya ta kwashe tana bin turbar dimukraɗiyya, inda ya ce a yanzu ƴan siyasa ba su da aƙida.

"Ai ba za ka taɓa haɗa ƴan siyasar yanzu da Sardauna ba ko Malam Aminu Kano ko Abubakar Rimi ko Janar T.Y Ɗanjuma ko kuma malam Adamu Ciroma ba. Su waɗannan sun yi siyasa ne domin bautata wa al'umma. Amma ƴan siyasar zamanin nan suna yi ne kawai domin kansu. Siyasar ta yanzu babu aƙida." In ji barista Mukhtari Shagari.

People are also reading