Home Back

Shin Arsenal Ta Barar Da Damarta Ta Lashe Firimiya?

leadership.ng 2024/5/17
Shin Arsenal Ta Barar Da Damarta Ta Lashe Firimiya?

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai ba su ji dadin sakamakon wasansu da kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa ba sai dai har yanzu magoya bayan suna da yakinin Arsenal din za ta iya lashe gasar har yanzu.

A ranar Lahadi ne dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta barar da damar hawa kan teburin Premier League, bayan da ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Aston Billa a filin wasa na Emirates. Aston Billa, karkashin tsohon kociyan Arsenal, Unai Emery ta doke

Arsenal gida da waje kenan a bana, bayan cin 1-0 ranar 9 ga  Disambar 2023 a filin wasa na Billa Park.

An kuma ci Arsenal kwallayen biyu dab da za a tashi ta hannun Leon Bailey a minti na 84 da Ollie Watkins saura minti uku a busa tashi kuma da wannan sakamakon Arsenal mai maki 71 iri daya da na Liberpool ta ukun teburi, Manchester City tana da maki 73 ta dayan teburi da tazarar maki biyu tsakaninsu.

Sai dai tun a ranar Asabar Manchester City ta dura 5-1 a ragar Luton Town a filin wasa na Etihad a ranar Crystal Palace ta ci Liberpool 1-0 a filin wasa na Anfield a karawar mako na 33. Wannan shi ne karon farko da aka ci kungiyar Arsenal a 2024 cikin wasa

11 a Premier League, wadda ta tashi ba ci da Manchester City, sannan ta lashe sauran wasannin gaba daya.

Rabon da Arsenal ta dauki gasar Premier League tun kakar wasa ta 2003 zuwa 2004 mai 13 jimilla, tun daga nan ba ta sake lashe kofin ba hakan ya sa magoya bayan kungiyar suke yunwar lashe gasar.

Kungiyar Arsenal ta kare kakar bara ba tare da daukar kofi ba, bayan da Manchester City ta sha gaban Arsenal a Premier daga karshe-karshen gasar sannan hakan ya bai wa Manchester City damar lashe kofi uku ciki har da na FA Cup da kuma KofinZakarun Turai karon farko a tarihi.

Saura wasanni shida da Arsenal za ta buga nan gaba, ciki har da karawa da Chelsea da Tottenham da kuma Manchester United, inda ake tunanin za ta iya sake barar da maki.

Wasannin da suke gaban Arsenal a Premier League:

20 ga Afirilu – Wolbes ( Molineud) 23 ga Afirilu – Chelsea (Emirates) 28 ga Afirilu – Tottenham (Tottenham Stadium) 4 ga Mayu – Bournemouth (Emirates) 12 ga Mayu- Manchester United (Old Trafford) 19 ga Mayu – Eberton (Emirate) Tasirin Magoya Baya

Bayan da kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa ta zura kwallo ta biyu a ragar Arsenal a filin wasa na Fly Emirates, magoya bayan kungiyar Arsenal sun dinga ficewa daga filin tun kafin alkalin wasa ya tashi daga wasan wanda hakan koma baya ne ga kokarin kungiyar na lashe gasar firimiya. Tsohon dan wasan Arsenal, Ian Right, ya soki matakin magoya bayan na ficewa daga filin tun kafin a tashi inda yace kwata-kwata bai kamata ba kuma hakan zai karyarwa da ‘yan wasa gwiwa. Right ya bayar da misali da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ba sa fita har sai alkalin wasa ya tashi daga wasa saboda suna ganin indai har ba a tashi ba tabbas ‘yan wasan kungiyar za su iya faranta musu rai ta hanyar zura kwallo a raga.

People are also reading