Home Back

Gimbiyoyin Kannywood (6)

leadership.ng 2024/7/1

Momee Gombe

Kannywood

Wata jarumar da tauraruwarta ke haskawa a masana’antar Kannywood ita ce, Momee Gombe, hakan ya sa muka saka ta a cikin gimbiyoyin Kannywood na wannan mako, jarumar ta lashe kyautar gwarzuwar jarumar mai tasowa a wani bikin karramawa da ‘Pandora Awards’ ta shirya a shekarar 2023, sakamakon wata waka da ta yi da mawaki, Hamisu Breaker mai suna ‘JARUMA’.

Momee ta fara harkar rawa da waka da manyan jarumai da suka hada da Garzali Miko, Umar M Sharif, Hamisu Breaker da sauransu, kafin daga bisani ta shigo masana’antar Kannywood gadan-gadan. Rawar da ta taka a cikin shiri mai dogon zango na ‘GIDAN SARAUTA’ da kamfanin ‘Mai Shadda Mobies’ yake shirya ya kara daukakata a idon duniya. Nasarar da Momee Gombe ta samu ya zamo manuniya ga kananan jarumai masu tasowa da yake nuna cewa kowa zai iya samun daukaka a harkar fim matukar ya jajirce.

Aisha Abdulrauf (Izzar So)

Kannywood

Aisha Izza kamar yadda aka fi saninta na daya daga cikin manyan jarumai mata da suka samu daukaka a cikin kankanin lokaci a masana’antar Kannywood, tun bayan fitowarta a cikin shiri mai dogon zango na ‘Izzar So’, Aisha ta samu daukaka a ciki da wajen Nijeriya saboda rawar da ta taka a cikin shirin wanda kamfanin Bakori TB ke dauki nauyi.

Yanayin rashin daukar raini da son girma da jarumar kan nuna a mafi yawancin fina-finanta yana matukar burge wasu daga cikin masoyanta, yayin da wasu kuma ke ganin cewar girman kai rawanin tsiya ne a kowane lokaci, amma duk da haka dai Aisha ta samu tagomashi tun bayan fitowarta a cikin shirin ‘Izzar So’.

People are also reading