Home Back

Naira Ta Gama Tashin Gishirin Andrew, Dalar Amurka Ta Sake Harbawa Najeriya

legit.ng 2024/5/17
  • Labaran da muka samu daga wurare dabam-dabam sun bayyana cewa kudin Najeriya watau Naira ya fadi a kasuwa
  • Kwanaki bayan Dalar Amurka ta fado sosai, sai aka ji Naira ta cigaba da rasa kimarta a kasuwar canji da kuma bankuna
  • ‘Yan kasuwar canji suna saida Dala a kan kusan N1, 400, wannan ya maida murnar da ‘yan Najeriya suka fara zuwa ciki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Daraja da kimar kudin Najeriya watau Naira yana ta karyewa bayan ana murnar ya farfado a can kwanakin baya.

Rahotanni sun bayyana cewa Dalar Amurka ta tashi a kasuwanni canji na bayan fage da kuma a hannun bankunan kasar.

Bayanan da aka samu daga shafin Naira Rates a shafin X da aka fi sani da Twitter ya nuna Dala ta dawo N1, 250.527.

A safiyar Juma’ar, an saida Pounds na Birtaniya a kan N1528 sai kuma kudin Euro na kasashen Turai a kan N1, 337.59.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta ce Naira ta karye zuwa N1, 320 a kan duk Dala zuwa tsakiyar makon nan.

Abin da hakan yake nufi shi ne kudin kasar na Naira ya karye da 1.54% daga N1, 300 da aka canji Dalar Amurka kafin yanzu.

A hannun ‘yan canji da ke kasuwannin BDC, an rika sayen Dala a kan kusan N1, 300 sannan a saida da ribar kusan N60.

A kafar FMDQ da ake cinikin kudin kasashen waje, an saye Dala ne a N1, 410 a jiya.

Rahoton ya ce ga masu bukatar sayen kudin kasar Amurkan, sai sun biya akalla N1, 051 zuwa yammacin ranar Juma’ar nan.

Kwanakin baya Dalar ta karye zuwa kusan N1, 000 a kasuwanni da bankuna, hakan ya sa aka fara tunanin farfadowar Naira.

Hakan ya sake jawo alamar tambaya a kan dabarun da Yemi Cordoso ya fito da su a CBN.

Wasu masanin tattalin arziki sun bayyana cewa dama zai yi wahala darajar Naira ta dade a haka, kimar kudin zai sake ruguzowa.

Asali: Legit.ng

People are also reading